Shugabannin Fulani daga sassa daban-daban na Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu a kafafen sadarwa na zamani, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar.
- Za mu hukunta duk wanda ya ki karbar tsoffin kudi —Ganduje
- Matawalle ya kori Kwamishinan Kudin Zamfara
Sanarwar ta ce shugabannin Fulani da ake kira da Ardo, sun bayyana goyon bayan ne a wani taro da suka gudanar a Abuja a ranar Lahadi.
A taron da suka yi tare da hadin kan kungiyar sabuwar Arewa wato “Arewa New Agenda” shugabannin sun yi alkawalin yin amfani da ’ya’yan kungiyar 33,661 wajen janyo kan sauran ’yan uwansu Fulani domin su zabi Tinubu a zaben da ke tafe.
A jawabinsa bayan an kammala al’adar Fulani ta rabon goro ga mahalarta taron, shugaban kungiyar, Aliyu Liman Bobboi, ya ce raba goron da aka yi yana nufin shugabannin za su koma gida su isar da sakon shawarar da aka yanke a wajen taron ga mabiyansu.
Ya kara da cewa, an gudanar da taron ne domin nuna wa duniya goyon bayansu ga Tinubu saboda sun yarda kuma sun yi amanna da cancantarsa, dalilin da suke masa addu’ar samun nasara a zabe mai zuwa.
Ya bayyana cewa a matsayinsu na shugabanni, suna da ta cewa sosai a kan wanda mutanensu za su zaba, kuma suna da yakinin cewa magoya bayan nasu za suyi masu biyayya.
Liman ya ce makusanta shakikai da ke tare da Tinubu kamar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa, tsohon shugaban EFCC Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan Fulani, wata manuniya ce ta yadda Tinubu ya dauki kabilar Fulani da muhimmanci.
An ba wa Tinubu sarauta
Kungiyar ta shugabannin Fulani ta kuma ba wa Tinubu sarautar Barkindo.
A jawabin Gwamna Ganduje, ya yi tsokaci kan irin bajinta da kwarewa da kuma cancantar Tinubu ta shugabancin Najeriya.
Ganduje ya ce Fulani a matsayinsu na kabila da ke fuskantar barazana a sassa daban daban-daban suna bukatar zabar shugaban da zai iya ba su kariya.
Ganduje ya kara da cewa, suna ci gaba da kokarin samar wa Fulani da wani tsari wanda zai bunkasa hanyoyin kiyo a duk fadin kasar nan.
A nasa jawabin, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Sanata Tinubu ya yi tsokaci a kan irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarsa a bangare daya da kuma Fulani a dayan bangaren.
Ya nuna cewa alakarsa da Fulani amana ce da ta kasance ta dindindin.
Ya kara jaddada aniyarsa ta samar wa Fulani hanyoyin kiyo na zamani da za su kawo ci gaba da kuma yalwa ba tare da tsangwama ba.
Tinubu ya kara da cewa, bai taba tsammanin zai hadu da bafulatanin da ya fi shi jin yaren yarbanci ba sai ga shi yau ba zato ba tsammani ya hadu dasu, yana mai cewa wannan abun a yaba ne.
“Wannan ita ce irin Najeriyar da muke bukata, kasa daya al’umma daya.
“Ina mai tabbatar muku idan da za mu kasance a nan tsawon sa’o’i biyar iyakacin dai zancen da za ku ci gaba da ji daga gare ni kenan.
“Ina mai matukar mika godiya da gareku.
“Tabbas makiyayan Najeriya na fama da matsaloli daban-daban amma ina mai tabbatar muku da cewa muna da tsari na musamman da zai magance wudannan matsalolin.
A nasa jawabin, Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ya cancanta ya dace wanda kuma zai iya kawo ci gaba mai dorewa ga kabilar ta Fulani.
Ya kuma yi godiya ga goyon bayan da suka ba shi tare da alkawalin ba zai ba su kunya ba.