✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna gargadin jam’iyyu a kan jinkirta fidda gwanayen takara —INEC

Duk wani zaben fidda gwanin da aka yi sabanin jadawalinmu ya zama haramtacce.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta gargadi jam’iyyun kasar da su tabbatar da kammala zaben fidda gwani na ’yan takarar zabe mai zuwa a cikin wata guda, ko kuwa ta haramta musu tsayar da ’yan takarar.

Daraktan wayar da kan jama’a dangane da shirin zaben Festus Okoye ya bayyana haka, inda yake cewa tun daga ranar 26 ga watan Fabarairu suka gabatar da shirin zaben shekarar 2023 wanda ya umurci jam’iyyun da su gudanar da zaben fidda gwani tsakanin ranakun 4 ga watan Afrilu zuwa 3 ga watan Yunin wannan shekara.

Okoye ya ce bisa wannan jadawali, duk wani zaben fidda gwanin da aka yi bayan wadannan ranaku ya zama haramtacce, kuma hukumar ba za ta amince da shi ba.

Daraktan ya ce sun shaidawa daukacin Jam‘iyyu 18 dake da rajista wannan doka kamar yadda Sashe na 82 na Dokar Zaben shekarar 2022 ya tanada.

Okoye ya ce tuni wasu daga cikin jam’iyyun suka fara shirin aiki da dokar, kuma Hukumar Zabe ta tura jami’anta domin sanya ido akan yadda suke gudanar da zaben.

Ana iya tuna cewa, saba wa Dokar Zabe wajen gudanar da zaben fidda gwani ya sa jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta rasa kujerar gwamna da ’yan majalisun tarayya da na jiha a zaben shekarar 2019.

%d bloggers like this: