Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ce sojoji na bukatar su kara nuna hazaka da kwarewa muddin ana so a kawo karshen matsalar tsaro a kasar.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake bude taron bayar da horo ga dakarun rundunar karo na 22 a Makarantar Samar da Kayan Aiki da Sufuri da ke Birnin Benin na Jihar Edo ranar Talata.
Kalaman nasa na zuwa ne kwana daya bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari Makarantar Horar da Sojoji ta NDA da ke Kaduna inda suka kashe sojoji sannan suka tafi da wasu.
A cewarsa, “Duk da karancin ma’aikatan da muke fuskanta, akwai bukatar a kara samar wa da dakarunmu kayan aiki.”
Horon dai na da taken: “Samar da ingantaccen horo ga sojojin kasa na Najeriya domin samun damar sauke nauyin da aka dora musu.”
Babban Hafsan ya kuma ce, “La’akari da yanayin da muke aiki a yanzu mai cike da tarin kalubale; aiki na yi wa ma’aikatanmu yawa, wanda hakan ke zuwa da sabbin kalubalen da ke bukatar nuna kwarewa.
“Saboda haka, akwai bukatar sojoji su ci gaba da jajircewa sannan su bullo da sabbin hanyoyin magance sabbin kalubale.
“Ina horonku da ku yi amfani da wannan horon wajen bullo da sabbin hanyoyin inganta harkokin tsaro a Najeriya,” inji Faruk Yahaya.
A cewarsa, a yanzu haka rundunar na gudanar da aikace-aikacen rundunoni iri-iri fiye da kowanne lokaci a baya, wanda hakan ya sa bukatar ma’aikata da kayan aiki ya dara na kowanne lokaci.