✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna fama da matsalar tsaro amma Tinubu ya tafi yawon buɗe ido — Atiku

Idan Tinubu ba zai iya jagorancin kasar ba ya matsa gefe.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da wasa da lamarin jagorancin kasar a yayin da ake fama da matsalar tsaro da tattalin arziki.

Atiku ya bayyana takaicin yadda a makon jiya Shugaba Tinubu ya fita ziyara ta kashin kai zuwa Faransa, lamarin da ya sanya tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ke zargin bai ɗauki jagorancin kasar da muhimmanci ba.

Atiku ya caccaki Tinubun ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya zargi shugaban da gazawa wurin jagorancin ƙasar.

“Tinubu ya tsaya wasa yayin da Nijeriya ke neman nutsewa cikin kogin rashin tsaro.

“Ina dalilin da babban kwamandan askarawa na ziyara wadda ba ta aiki ba a yayin da masu garkuwa da mutane suka kashe wata mai shayarwa da wata dattijuwa a Abuja kan gaza biyan kuɗin fansa har miliyan 90 da kuma wasu sarakai biyu a Jihar Ekiti, da wasu bala’o’i da ke faruwa a Nijeriya,” in ji Atiku.

“Idan takalman Emilokan sun yi masa girma, ya janye gefe saboda Nijeriya ba ta buƙatar shugaba ɗan yawon buɗe ido.

“Kasar nan tana bukatar jagoranci ba dare ba rana domin tunkarar matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki,” kamar yadda Atiku ya ƙara da cewa.

Sai dai kawo yanzu Fadar Shugaban Kasar ba ta mayar da martani kan zargin da Atiku yake yi wa Shugaba Tinubun ba.

Aminiya ta ruwaito cewa a Larabar makon jiya ce Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa domin wata ziyara ta ƙashin kansa.

Fadar Shugaban Kasar cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar ce ta bayyana hakan.

Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya ne a makon farko na watan Fabarairun 2024.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko tun bayan zaftare kashi 60 cikin 100 na adadin makarraban da za su rika yi wa Tinubun rakiyar tafiye-tafiye.