✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sojoji Suka Ceto Mutane 35 Daga Hannun ’Yan Ta’adda A Katsina

Wadanda aka ceton sun hada da kananan yara hudu, maza 19 da mata 12

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda sannan suka ceto wasu mutane 35 da a yi garkuwa da sau a Jihar Katsina.

Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji da ke Jihar Katshina, Kyaftin Yahaya Ibrahim, ya cewa wadanda aka ceton sun hada da maza 19 da mata 12 sai kananan yara hudu.

Kyaftin Yahaya Ibrahim, ya bayyana cewa a yayin ci gaba da kakkabe ’yan ta’adda ne sojojin suka yi arba da gungun ’yan ta’addan a maboyarsu da ke Dajin Dumburum a ranar Litinin.

A yayin musayar wuta aka kashe ’yan ta’adda biyu, ragowar kuma suka tsere da raunukan harbi a jikinsu.

Sanarwarsa ta ce tuni aka Kwamandan Birged na 17 da ke jihar, Birgediya OA Fadairo, ya mika wadanda ake ceton ga gwamnatin jihar ta Katsina.