Rundunar ’yan sanda ta Abuja ta ce tana ci gaba da binciken zargin kisan Bilyamin Mohammed Bello,dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Bello Halliru Mohammed wanda matarsa Maryam Sanda ta yi masa.
A tattaunawar da wakilin Aminiya ya yi da shi ta wayar salula jiya, Mai Magana da Yawun Rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da cewa wacce ake zargin ta aikata laifin tana hannu.