✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar taimakon makaranta – Nakasassun Borno

A karshen makon da ya gabata ne aka gudanar da bikin ranar nakasassu ta duniya wanda Majalisar dinkin Duniya ta ware don tuna wa nakasassun…

A karshen makon da ya gabata ne aka gudanar da bikin ranar nakasassu ta duniya wanda Majalisar dinkin Duniya ta ware don tuna wa nakasassun da kuma irin gudunmuwar da kowa zai iya bayarwa don ci gaban rayuwarsu da yadda su kansu yadda za su inganta rayuwar tasu.

Malam Umar Muhammad, Shugaban Gamayyar kungiyar Nakasassun Jihar Borno, ya fadi irin matsalolin da suke fuskanta a zantawar da ya yi da wakilinmu a garin Maiduguri, inda ya  ce “A gaskiya muna yi wa Majalisar dinkin Duniya godiya na yadda ta ware wannan rana don tunawa da mu, sannan kuma su ma kansu wadansu gwamnatocin jihohin na kasaar nan suna kokari wajen inganta rayuwar ‘yan uwanmu nakasassu, domin har kullum bukatarmu ya zo daidai ne da na gwamnati na cewa mu daina barace-barace a kan tituna, domin ya na zubar da kimarmu, kuma yana ci gaba da kawo mana mutuwar zuciya, duk da cewar ma a yanzu haka wasu masu lafiya din sun karbe mana sana’ar, amma mu yanzu muna kokarin tattara namu-ya namu mu kaurace wa baran matukar gwamntin Jihar Borno ta iya biya mana bukatunmu. 

“Na ji wasu jihohin tuni suka kauracewa sana’ar baran, to amma mu a yanzu haka mun fara duba yiwuwar bin hanyoyin kaurace wa baran domin kuwa baya ga samarwa da guragu sama da 50 aikin yin shara wanda Ma’aikatar tsaftace Muhalli ta gwamnatin jiha ta yi, akwai kuma wata Kamfanin Masana’antar Sarrafa kayayyakin bukatun yau da kullum na (DA’ISH) ya koya wa wasu nakasassu irinsu Mai, Sabulu, Turare, dinkin, kere-kere irin na zamani, da jima irin na zamani da dai sauransu.

“Wannan mutanenmu da yawansu ya kai har sama da 500, duk sun koya kuma a yanzu haka wasu suna nan suna koya, kuma na tabbata za su bai wa marada kunya.

“Akwai kuma wadansu da suke aikin kamasho a tashoshin motoci da kuma dai sauran, wadansu sana’o’in hannun da ‘yan uwanmu nakasassu za su ci abinci da shi. Kuma muna nan muna kokarin samarwa wasu sana’o’in hannun don dogaro da kai ta yadda za mu nisanci wannan baran da ake ta magana a kai, to amma mu a wannan lokacin muna bukatar tallafin gwamnatin Jihar Borno ta bangaren ilimi, wato ta kara yawan makarantun nakasassu a wannan jiha domin muna da makarantar koyon sana’’o’i ta makafi da ta kurame a hade kuma guda daya, ita ma din ba a kammala gyaran ta ba, to muna rokon gwamnatin jiha da ta gaggauta kammala gyaran wannan makaranta kuma ta kara mana wasu makarantun, sannan kuma ta samar mana da babban ofishi wanda za mu rika taruwa muna yanke shawarwari tare da yin wasu abubuwan da suka kamata, sannan kuma muna bukatar gwamnati ta samar mana da mota wanda za mu rika zirga-zirga.”