✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar taimakon abinci —Pakistan

Fiye da mutum dubu daya ambaliyar ruwan ta hallaka a kasar Pakistan.

Fira Ministan Pakistan, Shabaz Sharif, ya bukaci taimakon kasashen duniya bisa karancin abinci da al’ummar kasarsa ke fuskanta tun bayan mummunar ambaliyar ruwan sama da kasar ta fuskanta.

A yayin wata tattaunawa da Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya da yake masa godiya bisa tallafin abinci da tufafi gami da rumfuna, Fira Minista Sharif ya nuna kasarsa na bukatar samun taimakon gaggawa daga kasashen duniya.

Mutum sama da dubu 600 ne da suka hada da mata da kananan yara ke cikin yanayi na bukatar taimako sakamakon bala’in ambaliyar ruwa da ’yan kasar suka ce ba su taba ganin irinta ba.

Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji masu zaman kansu na ci gaba da fadi-tashin isar da kayayakin taimako ga al’ummar kasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, fiye da mutum dubu daya ambaliyar ruwan ta hallaka a kasar Pakistan a makonnin baya-bayan nan.