✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar N20bn domin gyara barnar ambaliyar Sakkwato – Tambuwal

Gwamnatin jihar Sakkwato ta ce tana bukatar sama da Naira biliyan 20 domin gyara barnar da ambaliyar ruwa ta haifar a 2020.

Gwamnatin jihar Sakkwato ta ce tana bukatar sama da Naira biliyan 20 domin gyara barnar da ambaliyar ruwa ta haifar a 2020.

Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal ne ya furta hakan ne a lokacin da yake karbar rahoto daga kwamimitin da ya kafa kan ambaliyar karkashin jagorancin Muhammad Jabbi Kilgori a dakin taro na fadar gidan gwamnatin jihar ranar Talata.

Ya ce ana bukatar biliyan 15 domin gina gadajoji da hanyoyi da ambaliyar ta lalata, sannan ana son sama da biliyan biyar domin tallafawa wadanda barnar ta shafa wadanda mafiyawansu manoma ne.

Tambuwal ya kuma ce duk abubuwan da suka lalace a ambaliyar da suka hada da dakunan shan magani da kananan asibitoci da hanyoyi da gadoji duk za a gyara a cikin kudin.

An kafa kwamitin ne wata daya da ya wuce saboda a gano cikakken bayani kan wadanda suka samu ambaliya da yawan dukiyar da ta salwanta da kayan da aka yi asara da kuma hanyoyin magance matsalolin da aka samu.

Tun da farko dai shugaban kwamitin Dakta Jabbi Kilgori ya ce sama da hekta 24,300 ne ruwa ya lalata bayan sun shafe harkokin noma da kiyo na dabbobi da kifaye da yawansu ya kai dubu 14.