✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna bincike a kan labarin mutuwar Shekau —Sojoji

Rahotannin mutuwar Shekau a hannun kungiyar ISWAP sun jawo ce-ce-kuce.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce har yanzu ba ta da tabbaci a kan labarin mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Ya zuwa yanzu ba a san inda Shekau yake ba tun bayan da rahotanni suka bayyana cewa ya mutu sakamakon gwabza wani kazamin fada da aka yi tsakanin Boko Haram da mayakan kungiyar ISWAP mai mubaya’a ga IS.

Rahotanni sun bayyana mutuwar Shekau a fadan da ya barke da Dajin Sambisa da ke Jihar Borno.

Sai dai yayin hirarsa da manema labarai, mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Mohammed Yerima, ya ce suna ci gaba da bincike a kan lamarin domin kuwa ba su da kwakkwarar hujja game da mutuwar tasa.

Majiyoyin tsaro sun ce Shekau ya kashe kansa ne ta hanyar kunar bakin wake bayan mayakan ISWAP sun kama shi suka kuma nemi ya sauka daga mukaminsa.

Wasu majiyoyin tsaro sun ce yunkurin nasa ba kai ga mutuwa ba amma ya samu mummunan rauni.

Wasu majiyoyin kuma sun ambato masu kusanci da kungiyar na cewa harbin kansa ya yi da nufin kashe kansa, amma kuma bai mutu ba.

Labarin yiwuwar mutuwar Shekau ya haifar da ce-ce-kuce daga bangarori daban-daban.

Abun damuwa

A tattaunawarsa da Aminiya, wani masanin harkar tsaro, Kabiru Adamu, ya ce bai kamata a yi la’akari da cewa an kashe Shekau ba, kamata ya yi a maida hankali kan yadda ISWAP ke kara karfi.

“Wannan na nufin rundunar soji na kara ba wa ISWAP dama wajen kara yin karfi.

“Zai kuma iya zama sako mara dadi ga jama’a kan yadda ake yaki da ta’addanci, idan aka tafi a haka zai zama tamkar sun fi karfin sojoji,” inji Kabiru Adamu.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar Tsaro, Birigediya Bernard Onyeuko, ya shaida wa wakilinmu ta rubutaccen sakon waya cewar “Ka yi hakuri, ba ni da masaniya kan hakan”.

Tuni dai labarin rasuwa Shekau ya dauki dumi, inda masu sharhi kan harkar tsaro suka shiga tofa albakacin bakinsu.