Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya ce yana bin Gwamnatin Tarayya bashi da ya kai Naira tiriliyan 2.8 na tallafin man fetur da ba ta biya ba.
Shugaban kamfanin na kasa, Mele Kyari ne ya sanar da hakan ranar Talata, yayin da yake zantawa da ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa, bayan zantawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 25 a kauyen Zamfara
- Matakin gwamnati na hana malaman jami’a albashi yana kan ka’ida – Kotu
Kyari ya kuma ce sun yi maraba da matakin da Shugaba Tinubu ya dauka a cikin jawabinsa na karbar mulki kan janye tallafin man fetur, inda ya ce ci gaba da bayar da tallafin ba abu ne mai dorewa ba.
Ya ce dimbin kudaden da ake kashewa sun sa kamfanin ba ya iya gudanar da ainihin ayyukan da ke wuyansa.
Mele Kyari ya ce ba su yi mamakin ganin dogayen layukan da suka sake bulla a gidajen mai ba tun ranar Litinin, saboda dillalan man za su so samun karin bayani kan kalaman Shugaban Kasa cewa “zamanin biyan tallafin mai ya shude”.
Sai dai ya ce gwamnatin za ta fito da matakan rage radadin da janye tallafin zai shafi mutane.
Ya kuma ce, “Tun bayan Naira tiriliyan shida da aka biya a 2022 da kuma Naira Tiriliyan 3.7 a 2023, ba mu karbi kowanne irin tallafi daga gwamnati ba.
“Hakan na nufin tun da gwamnati ta ki biyan wadancan kudaden, mu ne muka ci gaba da biya daga aljihunmu. Idan kudaden suka taru suka yi yawa, fargabarmu ita ce hakan zai gurgunta ayyukanmu a matsayin kamfani.
“yanzu haka muna jiransu su biya mu wannan bashin na tiriliyan 2.8, saboda ba za mu iya ci gaba da wannan aikin ba,” in ji Kyari.