✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakin gwamnati na hana malaman jami’a albashi yana kan ka’ida – Kotu

Sai dai ta ce gwamnati ba ta da hurumin kakaba musu shiga IPPIS

Kotun Ma’aikata ta Tarayya ta tabbatar da halaccin matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na hana malaman jami’o’i albashinsu a watannin da ba su yi aiki ba.

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ce dai ta daukaka karar tana neman a soke hukuncin da kotun baya ta yanke na goyon bayan gwamnati.

A hukuncin da Alkalin Kotun, Mai Shari’a Benedict Kanyip ya yanke ranar Talata, ya ce matakin da gwamnatin ta dauka na hana su albashi a watannin da ba su yi aiki ba lokacin yajin aikin daidai ne.

Kotun ta ce gwamnatin na da damar ta rike albashin duk wani ma’aikacin da ya tafi yajin aiki.

Sai dai kotun ta ce tilasta wa malaman jami’o’in su shiga tsarin biyan albashi na bai-daya na IPPIS ya saba wa ’yancin cin gashin kan jami’o’i a Najeriya.

Kazalika, kotun ta ce jami’o’in na da damar fayyace yadda za ta biya albashin ma’aikatansu.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairun bara ce dai ASUU ta tsunduma yajin aikin da ta shafe tsawon wata takwas don tilasta wa gwamnatin ta biya mata bukatunta.

Yajin aikin dai ya tilasta wa daliban Najeriya da dama dai zama a gida, inda gwamnatin ta ce ba za ta biya su albashin watannin da suka shafe suna yajin aikin ba.