✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 25 a kauyen Zamfara 

Daga cikinsu har da wani kwamandan 'yan sa-kai

’Yan bindiga sun kashe mutum 25 a wasu hare-hare guda uku da suka kai gundumar Kanoma da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa daga cikin mutanen da maharan da ke dauke da muggan makamai suka kashe, har da wani shahararren kwamandan ’yan sa-kai a yankin mai suna Dahiru Dangamji a wasu mataimakansa su uku.

An kashe ’yan sa-kan ne a wani daji mai nisan kilomita biyar, Kudu da garin na Kanoma.

Wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Aliyu, ya ce dama maharan sun dade suna fakon kwamandan da yaransa.

“Lokacin da labarin kashe kwamandan ya bulla a garin, sai ’yan sa-kai da dama dauke da makamai suka shiga dajin da nufin yin ramuwar gayya kan kisan jagoran nasu.

“Amma da ’yan bindigar da suka samu labarin hakan sai suka yi kwanton bauna, inda suka harbe 16 daga cikinsu. Amma su ma ’yan bindigar an kashe musu mutane, wata ruwayar na cewa sama da mutum 110, amma babu wanda zai iya tantance gaskiyar haka.

“Daga nan ne maharan suka wuce wajen hakar ma’adinai da ke kauyen Danzara, inda suka harbe masu hakar mutum biyar. Yanzu haka ana ta kokarin neman gawarwakin masu hakar ma’adinan da ’yan sa-kan domin a yi musu jana’iza.

“Maganar da nake da kai yanzu haka hankulan mutanen Kanoma a tashe suke, saboda an hangi ’yan ta’addan dauke da makamai suna kokarin shiga garin, watakila saboda su kai hari. Muna kira ga jami’an tsaro da su kawo mana dauki,” in ji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Yazeed Abubakar bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa don jin ta bakin rundunar a kan batun ba.