✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da Kanawa ke son Abba Gida-Gida ya aiwatar

A ranar Litinin aka rantsar da sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya gaji Abdullahi Umar Ganduje bayan kammala wa’adin mulkin shekaru hudu…

A ranar Litinin aka rantsar da sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya gaji Abdullahi Umar Ganduje bayan kammala wa’adin mulkin shekaru hudu karo biyu.

Aminiya ta zanta da mazauna jihar, inda suka bayyana abubuwan da suke so sabon gwamnan ya yi musu da zarar ya akalar jagoranci ta koma hannunsa.