Uwargidan tsohon Shugaban Najeriya Dame Patience Jonathan, ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu za ta marawa baya a Zaɓen 2027.
Patience ta nanata cewa ba ta da burin komawa fadar shugaban ƙasa, amma ta ce a shirye take ta taimakawa uwargidan shugaban ƙasa na yanzu, Sanata Oluremi Tinubu wajen yaƙin zaɓen 2027.
- Muhawarar da ta ɓarke kan saya wa Sarkin Kano motocin naira miliyan 670
- Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin
Aminiya ta ruwaito Patience na bayyana haka ne a lokacin da take kiran sunan manyan baƙi ciki har da ’yar shugaban ƙasar, Folashade Tinubu-Ojo a wajen taron da aka karrama ta a matsayin jagora ta gari, wanda kamfanin Accolade Dynamics Limited ya shirya ranar Asabar a Abuja.
Ta ce, “ita ya kamata in fara kira amma sai na bari zuwa ƙarshe wato ’yar shugaban ƙasarmu wanda muka aminta da shi wato Shugaba Bola Tinubu.
“Iyajola ina miki godiya bisa yadda kike ƙarfafa gwiwar mata. Muna tare da ke a wannan aikin kuma za mu mara miki baya.
“Ina da yawan magana, idan ba na son abu ana ganewa, amma idan ina tare da abu, zan iya mutuwa a kansa.
“Kowa da lokacinsa a mulki, kuma idan lokacin mutum ne, ina goya masa baya ne.”
Ta ƙara da cewa a lokacin da suke mulki, Uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu ta goya mata baya.
“Ina da hankali, don haka dole ne in mayar da biki. Na faɗa mata cewa zan taya ta yaƙin zaɓe, ba zan juya mata baya ba. Ni ba na sha’awar komawa fadar shugaban.”