Ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta yi Allah-wadai da harin da wasu ’yan bindiga suka kai a barikin soja da kuma gidajen yari a ƙasar Saliyo a ranar Lahadi.
ECOWAS ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi cewa; “Ta samu labarin wata maƙarƙashiyar da wasu mutane ke yi na sayen makamai da nufin kawo cikas ga zaman lafiya da mulkin dimokuradiyya a kasar.
“ECOWAS ta yi kakkausar suka ga wannan aika-aika kuma tana kira a gaggauta kamawa tare da gurfanar da duk masu hannu a cikin wannan haramtaccen lamari a gaban kotu.”
Har zuwa yanzu dai, mahukuntan Saliyo ba su fito kai tsaye sun bayyana takamaimai manufar masu kai hare-haren na ranar Lahadi ba.
Duk da haka ECOWAS ta nanata cewa ba za ta “lamunci duk wani sauyin gwamnati da ba ta hanyar da tsarin mulki ya tanada ba,” in ji sanarwar.
Ta kuma ce ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta kare tsarin dimokradiyya da inganta harkokin mulki, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da bunƙasa zamantakewa da kuma harkokin tattalin arzikin ƙasar Saliyo.
ECOWAS ta ce tana ci gaba da taka-tsantsan wajen kiyaye zaman lafiya da kimar dimokuradiyyar kasashe mambobinta.
Saliyo ta yi wa dokar takaita zirga-zirga kwaskwarima
Ƙasar Saliyo ta ɗage dokar takaita zirga-zirga ta sai baba ta gani da ta saka a faɗin ƙasar a ranar Lahadi bayan da wasu sanye da kakin sojoji suka kai hari barikin sojoji da kuma kuma gidajen yari.
Yanzu, dokar hana zirga-zirgar za ta fara aiki daga karfe 9 na dare zuwa 6 na safe agogon ƙasar har sai abin da hali ya yi.
Shugaba Julius Maada Bio, ya yi wa ’yan ƙasar jawabi , inda ya ce an kama yawancin shugabannin da suka kai harin kuma za a tuhume su, lamarin da ya sa hankula suka soma kwanciya a ƙasar.
Mista Bio ya kwatanta al’amarin a matsayin hari kan dimokuraɗiyya, sai dai bai bayyana sunayen mutanen ba ko kuma magana kan yunkurin juyin mulki.
Tun da farko a ranar Lahadi, gwamnatin ƙasar ta Saliyo ta ɗora laifi kan wasu sojoji saboda sun yi yunkurin kutsawa cikin barikin.
Ana kyautata zaton cewa waɗanda suka kai harin sun saki wasu furusnoni tare da yin garkuwa da wasu.
An sake zaɓar Shugaba Bio a watan Yuni, sai dai a watan Agusta aka kama wasu sojoji, inda aka zarge su da makarkashiyar kifar da gwamnati.