Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ware wa yankin Arewacin kasar kujerar shugaban jam’iyyar na kasa yayin da ake tunkarar babban zabe na 2023.
Gwamnan Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai da takwaransa na Jihar Kebbi Atiku Bagudu ne suka fada wa manema labarai, jim kadan bayan ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Talata.
- Dakarun Rasha sun shiga Ukraine da tankunan yaki
- Mataimakin gwamnan Zamfara ya ki bayyana gaban kwamitin da ke bincikarsa
El-Rufai ya ce jam’iyyar ta amince ta rarraba mukaman da babu kowa a kai a Kwamatin Koli na jam’iyyar tsakanin Kudu da Arewa kafin babban taronta na ƙasa.
Hakan na nufin mukamin shugabancin wanda John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole suka rike a baya, dukkansu ’yan Kudu, zai koma Arewa.
“Mun amince da wani tsari na karkasa mukamai ga dukkan shiyyoyin siyasa. Shiyyoyin Arewa za su samu mukaman da na Kudu suka riƙe a cikin shekara takwas da suka wuce, su ma (na Kudu) haka,” a cewar Gwamna El-Rufai.
Yayin taron, gwamnonin jam’iyyar ta APC sun amince da sabon lokacin da jam’iyyar ta zaba don gudanar da babban taronta na kasa duk da cewa an samu rabuwar kai tsakaninsu.
Gwamna El-Rufai ya ce ba zai yiwu a tara gwamnoni har 22 ba “kuma a ce ba a samu bambancin ra’ayi ba.”
Ranar Litinin ne kwamatin riko na shugabancin jam’iyyar ya bayyana cewa ya fasa gudanar da babban taron a ranar 26 ga watan Fabarairu sannan ya mayar da shi 28 ga Maris.
“An samu bambancin ra’ayi tsakanin gwamnonin APC game da lokacin taron,” in ji El-Rufai kamar yadda mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan kafafen sada zumunta Tolu Ogunlesi ya ruwaito shi yana fada.
Ya kara da cewa: “Wannan kuma wai shi ’yan jarida ke kira gwamnoni marasa hadin kai.
“Babu yadda za a yi a tara gwamnoni 22 kuma kowa ya amince da kowane irin kudiri. Za a iya samun bambanci amma idan aka kira shi rabuwar kai to an wuce gona da iri.”
Takaitaccen taron wanda ya gudana a dakin taro na Council Chambers da ke Fadar Gwamnatin Najeriya ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Gwamnonin APC 19 da suka hada da na Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Jigawa, Legas, Imo, Ogun, Borno, Neja, Gombe, Osun, Kebbi, Filato da kuma Mataimakin Gwamnan Anambra wanda ya koma jam’iyyar daga APGA a bara.