✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun tsiyace, kasafin kudin da ake ware mana ya yi karanci — Majalisa

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta sanar da cewa a halin yanzu ta tsiyace kuma ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin gudanar da…

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta sanar da cewa a halin yanzu ta tsiyace kuma ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin gudanar da ayyukanta kamar yadda ya kamata ba.

Mai magana da yawun Majalisar, Honarabul Benjamin Kalu na jam’iyyar APC, shi ne ya yi furucin hakan yayin zanta wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

Dan majalisar ya ce akwai bukatar a sake nazari a kan kasafin kudin majalisar domin rubanya mata shi da wani kaso wanda hakan zai ba ta damar shawo kan lamarin da ta tsinci kanta a cikinsa.

“Lallai tabbas Majalisar ta tsiyace, na sha fada a baya kuma ina sake fada don bana tsoron fadin hakan.”

“Wannan ita ce gaskiyar da har sai ’yan Najeriya sun yarda cewa kason da aka ware wa majalisar dokokin tarayya domin gudanar da harkokinta an yi ne a lokacin da darajar Dala daya tana daidai da Naira 180.”

“A yanzu Dala daya ita ce kwatankwacin fiye da Naira 400 wanda ya nuna kasafin kudin majalisar ya ragu fiye da yadda ya kasance shekaru 10 da suka gabata,” in ji shi.

Honarabul Kalu ya ce ya sha samun sabanin da Shugabannin Majalisar dangane da wannan lamari kuma a kullum tambayarsa ita neman dalilin da ba za a yi wa majalisar kari a kasafin kudin gudanar da harkokinta ba.

Ya ce, “ina dalilin ware wa hukumomi da cibiyoyin gwamnatin daban-daban isassun kudin gudanar da harkokinsu yadda ya dace amma muna jin tsoron yi wa namu kasafin kudin kari.”

“Wannan koma baya ne ga ’yan Najeriya duba da cewa nauyin hidimta musu ya rataya a wuyanmu,” a cewarsa.

Kazalika, ya yi bayanin cewa, kasafi Naira biliyan 128 da aka ware wa Majalisar Dokokin Tarayya ana kasafta shi ne a tsakanin dukkanin hukomin da ke Majalisar mai dauke da mambobi dubu shida na ma’aikata da hadimansu.

Ya ce ’yan majalisar suna bukatar yin aiki tare da kwararru domin shimfida dokoki da za su dace da bukatun al’umma yana mai cewa, “idan kuka duba kasar Amurka, za ku ga cewa Farfesoshi ne abokan huldar ’yan majalisa wadanda suke tuntube da aiki tare.”