Dan takara shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce yana tattaunawa da takwaransa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi domin yiwuwar hada gwiwa a Zaben 2023.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da BBC Hausa.
- Zaben Ekiti: SDP ta yi watsi da sakamako, za ta garzaya kotu
- Ta ina Arewa ta amfana da Gwamnatin Buhari?
A cewarsa “gaskiya muna magana da shi Peter Obi, ko kuma ma in ce kwamiti yana aiki domin ya duba dukkan abin da ya kamata (kan hada gwiwa da shi), kuma abokai da ’yan uwa suna zuwa suna yi mana magana kan batun.”
Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce hada gwiwarsu tana da muhimmanci musamman ganin cewa jam’iyyun APC da PDP ba su tsayar da dan takarar mataimakin shugaban kasa daga yankin kabilar Ibo ba.
Sai dangane da batun wanda zai zama mataimaki a tsakaninsu, Kwankwaso ya ce “to dai za mu duba mu gani, wanda yake babba shi zai ja ragama, wanda kuma yake karami sai ya zo a matsayin mataimaki.”
Da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho a ranar Lahadi, mai magana da yawun jam’iyyar NNPP na kasa, Dokta Agbo Major, ya ce duk wata shawara da aka yanke a karshen tattaunawar za ta yi wa ’yan Najeriya dadi.
“Da zarar mun kammala tattaunawa a kan batun hadin gwiwa da wanda zai zama jigon takara ko mataimaki, duk wani hukunci da aka yanke zai faranta wa ’yan Najeriya.”
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya zabi Doyin Okupe a matsayin mataimakinsa na riko kafin ya yanke shawarar wanda zai zaba.
Kazalika, Kwankwaso ya mika sunan wani lauya dan Jihar Legas, Barista Ladipo Johnson, a matsayin abokin takararsa a Zaben 2023.
Duka dai masu neman kujerar Shugaban Kasar sun mika sunayen ne ga Hukumar Zabe ta kasa INEC yayin da wa’adin da ta bai wa jam’iyyu ya kare a ranar Juma’a.