✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Mun shawo kan ’yan bindiga a kan kashe daliban jami’ar Greenfield’

Sako daliban Afaka ta kara mana karfin gwiwar ci gaba da tattaunawa da ’yan bindiga.

Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ’yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna sun fasa kashe su sabanin barazanar yin hakan da suka yi a baya.

Shehin malamin ya ce a yanzu sun shawo kan ’yan bindigar wajen sauke su daga ra’ayin da suka rika na kashe daliban da ke hannunsu muddin aka gaza cika sharadin biyan kudin fansa na naira miliyan dari da suka gindaya.

Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun yi barazanar ci gaba da yi wa daliban kisan dauki dai-dai muddin aka gaza biyan kudin fansa na naira miliyan dari da doriyar babura guda goma.

Sai dai a yayin tattaunawarsa a ranar Alhamis tare da iyayen daliban Kwalejin Harkokin Noma da Gandun Daji ta Afaka da aka sako, Sheikh Gumi ya ce tattaunawa na ci gaba gudana don ganin daliban jami’ar sun kubuta.

A cewarsa, sako daliban Afaka ta kara musu karfin gwiwar ci gaba da tattaunawa da neman sulhu da ’yan bindiga.

Ana iya tuna cewa, Sheikh Gumi da tsohon Shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ne suka shiga-suka-fita wajen kubutar da daliban Kwalejin Afaka.

“Har yanzu muna tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da daliban jami’ar Greenfield. Kun san akwai wani lokaci da suka yi barazanar kashe su gabata daya amma bayan mun maganar da muka yi da su, sun sauko daga wannan ra’ayin.

“Rawar da ni da tsohon Shugaban Kasa Obasanjo muka taka wajen sako ragowar dalibai 27 na Kwaleji Afaka mun yi a matsayin masu sulhu don saboda ba da mu suke yaki ba, fada ne tsakin ’yan bindiga da kuma gwamnati.

“Abin da muka fahimta shi ne cewa wannan mutan suna kokarin yakar gwamnati ne ta hanyar kai wa makarantun gwamnati hari sannan su debi daliban da babu ruwansu.

“Saboda haka muka ga ya dace mu shiga lamarin domin kubutar da wadannan dalibai duk da cewa ba lamari ba ne mai sauki,” a cewarsa.