✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun mayar da kidayar jama’a watan Mayu – Gwamnatin Tarayya

Ministan Yada Labarai ne ya sanar da hakan a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce kidayar jama’ar da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Maris, 2023, yanzu an mayar da ita watan Mayu.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa, jim kadan da kammala taron Majalisar Zartarwa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

Ya ce an yanke shawarar ce bayan dage zaben Gwamnoni da na ’yan majalisun Jihohi zuwa ranar 18 ga watan Maris.

Minstan ya kuma ce majalisar ta amince wa Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta kashe Naira biliyan biyu da miliyan 800 domin sayo wasu manhajoji da za a yi amfani da su a yayin aikin kidayar.

Lai Mohammed ya ce akwai wata bukata da Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta gabatar da take bukatar sayen wasu manhajojin da za su ba su damar gudanar da kidayar a watan Mayu mai zuwa. Na tabbatar dage zaben da aka yi ya sa ba za su iya gudanar da kidayar ba kamar yadda aka tsara tun da farko.

“Sun bukaci a sahale musu su kashe Naira biliyan biyu da miliyan 800 domin sayen wasu manhajoji,” in ji Ministan.