Tsohon Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Lai Mohammed, ya bayyana yadda labaran karya a shafukan sada zumunta suka kusa kashe masa auren shekara 40 da matarsa.
Da yake jawabi a wajen bikin cikar Farfesa Wole Soyinka shekara 90 a duniya, Mohammed ya bayyana yadda labaran karya suka yi tasiri lokacin da yake minista.
- ’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Kaduna
- Ina cikin takaici kan irin abincin azumi da ake raba wa Kanawa — Gwamnan Kano
Mohammed ya bayyana yadda matarsa a 2018 ta taba tashinsa cikin dare domin tattauna wani batu wanda gaba daya labarin karya ne.
“Cikin dare wata rana na dawo daga Legas zuwa Abuja, bayan wani aiki ina tsaka da barci matata ta tashi wai tana so mu tattauna wani abu mai muhimmanci.
“Kawai sai ta ce min wai mutuwa na iya zuwa kowane lokaci, don haka na ba ta dama ta zama daya daga cikin wadanda za su iya cire kudi daga asusuna da ke kasar waje mai dala biliyan 1.3.
“Na shafe sama da sa’o’i biyu ina gumi, ina mata jawabin yadda za ta fahimce ni amma abun ya ci tura,” in ji shi.
Duk da kokarin da ya yi na bayyana wa matarsa rashin ingancin labarin amma ta ki yarda.
Tsohon ministan ya yi mata jawabi dalla-dalla don tabbatar da cewa ba shi da hannu a kudin da ake zargin nasa ne, wanda ta kai sa ga yi wa matar bayanin yadd kasafin kudin Najeriya yake domin saukin fahimta.
Sai dai ya ce duk da haka, a gefe guda kawayen matarsa sun yarda da labarin, inda wasu ke kallon sa a matsayin barawon gwamnati.
Mohammed ya yi Allah-wadai da yadda labaran karya ke kara yawaita a shafukan sada zumunta, inda ya bayar da misalin irin karairayin da aka yi wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma shugaba Bola Tinubu.
Tsohon ministan ya yi gargadi kan irin illar da ke tattare da yada labaran karya, wanda a cewarsa za su iya gurgunta tsarin dimokuradiyya da tsaron jama’a a kasar nan.
Ya bukaci masu kafafen watsa labarai da suke yin kokarin wajen tabbatar da ingancin labarai kafin yada su, domin za su iya tasiri ga rayuwar jama’a da makomar kasar nan baki daya.