Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ce Shugaban Kasa Bola Tinubu ne da kansa zai bayyana sabbin ranakun da za a gudanar da kidayar jama’a da gidaje a Najeriya.
Shugaban hukumar, Nasir Isah Kwarra ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan ya jagoranci tawagar hukumar domin yin bayanin inda suka kwana ga Shugaba Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja.
- Majalisar Dattawa ta soki Gwamnatin Buhari kan jinginar da tashar jiragen sama
- INEC ta maka wanda ya ce Binani ce ta lashe zaben Gwamnan Adamawa a kotu
Ya ce ya zuwa yanzu, hukumar ta mika rahotonta ga Shugaban, kuma shi take jira ya yi nazari a kai sannan ya yanke hukunci kan lokacin da za a gudanar da ita.
Sai dai ya ce saboda tsawon lokacin da ake dauka, bukatun hukumar na karuwa, don haka akwai yuwuwar su bukaci karin kudi a nan gaba.
Ya ce, “Mun yi masa cikakken bayani a kan shirye-shiryenmu, kuma muna farin ciki Shugaban ya nuna a shirye yake ya tallafa wa dukka tsare-tsarenmu 100 bisa 100 kan dukka bukatunmu.
“Saboda haka, mu za mu je mu ci gaba da shirye-shiryenmu, kuma za a ji daga bakinsa, ranakun da za a yi kidayar a nan gaba, saboda mu mun riga mun mika masa rahoto, zai kuma yi nazari a kai.
“Amma dai ya ba mu tabbacin tallafa mana, kuma muna gode masa a kan haka, musamman la’akari da muhimmancin kidaya wajen tsare-tsaren ci gaban kasa,” in ji Nasiru Kwarra.