Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta ce ta kwato kudi sama da Naira biliyan 30 daga cikin biliyan N109 da ake zargin tsohon Akanta-Janar na Kasa, Ahmed Idris, ya yi sama da fadi da su.
Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, ya ce kafin karshen shekara, hukumar za ta yi wa ’yan Najeriya gwanjon wasu rukunin gidaje da wasu dukiyoyi masu tarin yawa da hukumar ta kwato daga barayin dukiyar kasa.
- APC Ta Karbi Daruruwan Magoya Bayan PDP a Katsina
- Kotu ta kwace masallatai da litattafan Abduljabbar
Da yake bayani a ranar Alhamis, a taron mako-mako da suke yi kan ayyukan hukumar, shugaban na EFCC ya ce cikin tsarinsu na gano hada-hadar kudi, nan da shekara uku zai yi wuya a iya karkatar da dukiyar kasa zuwa wani asusun banki.
Bawa, ya yi karin haske kan ayyukan hukumar tare da irin fadi-tashin da take yi wajen yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa.
Tun da farko dai, Akanta-Janar Ahmed Idris an zarge shi da yin sama da fadi da kudi biliyan 109 daga ofishin gwamnati.
Daga bisani EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu inda aka aike shi zuwa gidan yari.
Amma daga baya ya samu beli, wanda tun daga wancan lokaci ake ci gaba da shari’a kan almundahanar da ake zargin sa da aikatawa.