Zababben Dan Majalisar Tarayya a Jam’iyyar NNPP, Abdulmuminu Jibrin Kofa, ya ce ficewarsu daga Jam’iyyar APC ya koya wa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, darasin siyasa.
Kofa, ya bayyana haka ne cikin wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
- ’Yan sandan Isra’ila sun fatattaki Musulmi masu ibada a masallacin birnin Kudus
- Mun karbo bashin $800m don rage radadin tallafin man da za mu cire – Gwamnati
Jam’iyyar NNPP ta kayar da APC mai mulkin jihar a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
“Mun tabbatar da cewa ba sake motsawa ba a APC, a karshe ya ja musu asarar ’yan majalisar tarayya 18 ciki har da mutum bakwai da kasar nan za ta iya tunkaho da su.
“Ya sanya sun rasa kujerun ’yan majalisar jiha 34; Ina tabbatar maka da cewar wasu daga cikinsu suna da nagarta. Amma sun fadi ne saboda Ganduje.”
Sai dai tun bayan faduwar jam’iyyar APC zaben gwamna a jihar, jam’iyyar ta kuduri aniyar zuwa kotu don kalubalantar sakamakon.
Tun da fari jam’iyyar ta ce zaben gwamnan kamata ya yi a ayyana shi a matsayin bai kammala ba.