✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun kori Sheikh Nuru Khalid daga limanci gaba daya —Sanata Dansadau

Sanata Dansaudau ya ce martanin da Sheikh Nuru Khalid ya mayar ya nuna bai yi nadama ba.

Kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen ’Yan Majalisar Tarayya na Apo, ya ce ya kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba daya.

Shugaban Kwamitin, Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau ne ya bayyana wannan sabon mataki yayin zantawa da BBC wanda ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid a ranar Asabar ta gabata.

Tun da farko dai an dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci ne bayan wata zazzafar hudubar da ya yi inda ya caccaki gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan matsalar tsaro.

Aminiya ta ruwaito cewa, a cikin hudubarsa ta ranar Juma’ar da ta gabata, Sheik Nuru Khalid ya caccaki gwamnati kan gaza magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya, inda ya yi kira ga al’ummar kasar da su kaurace wa babban zabe da ke tafe muddin ba a magance matsalar tsaron ba.

“Sharadin talakan Najeriya ya zama guda daya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zabe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,” inji Sheikh Nuru Khalid a hudubar tasa.

Wannan hudubar ce silar dakatar da Sheikh Khalid daga limanci, inda bayan kwana daya ya mayar da martani inda ya wallafa wata ayar Alkur’ani mai cewa: “Allah Shi ne mafi girma. Shi ke ba da mulki ga wanda Ya so, kuma Ya kwace daga wanda Ya so.”

“Ya Allah, Kai ne mai girma da daukaka, Kai ke ba da mulki ga wanda Ka so, Ka kwace daga wanda Ka so, Ka daukaka wanda Ka so, kuma Ka kaskantar da wanda Ka so. Dukkan alheri a hannunKa yake, Kai ne mai iko a kan komai,” kamar yadda ya wallafa.

Sai dai cikin wata wasika da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun Sanata Dansadau, ta ce a yanzu an dauki matakin korarsa gaba daya saboda kin yin nadamar da ya nuna bayan dakatar da shi da aka yi.

Wasikar ta ce: “Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara dabi’ar mutum.

“Abin takaici, martanin da ka mayar kan dakatarwarka ta nuna cewa, balle ma har ka nuna nadama kan abubuwan da ka fada.

“Shugabanci na bukatar sauke hakki ka’in da na’in. Idan kalamanmu sun bata wa ’yan kasa rai fiye da faranta musu, to akwai hakki a kanmu na daukar matakin da ya dace saboda al’umma.

“Ga dukkan alamu kuma kamar ba ka da niyyar gyara hudubarka ta ranar Juma’a ta yadda za ta yi daidai da halin rashin tsaro da ake ciki a Najeriya,” in ji sanarwar.

%d bloggers like this: