Rundunar Sojin Najeriya, ta bayyana cewar ta kashe ’yan ta’adda 10,937 a shekarar 2024 da aka yi bankwana da ita.
Rundunar ta kama mutum 12,538 tare da ceto 7,063 daga hannun ’yan ta’adda a wasu samame da suka kai daban-daban a faɗin ƙasar.
- 2025: Tinubu ya aike wa ’yan Najeriya saƙon fatan alheri
- ’Yan bindiga sun sace fasinjoji, sun ƙone mota a Zamfara
Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na Rundunar, Manjo Janar Edward Bubaya ne, bayyana wannan a taron manema labarai da aka yi a Abuja.
Ya jaddada cewa sojojin sun rage ƙarfin ’yan ta’adda sosai, inda 16,171 daga cikinsu da iyalansu suka miƙa wuya.
Buba, ya kuma bayyana cewa sun ƙwato makamai nau’i daban-daban, ciki har da bindigogi 8,815 da muggan makamai 228,000.
“Mun hana masu satar man fetur samun kuɗaɗen da suka kai kimanin Naira biliyan 68.4 a tsawon wannan lokaci,” in ji Buba.
A yankin Arewa maso Gabas, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 3,151, sun kama masu laifi 2,503, sannan sun ceto mutanen da aka sace 1,605.
Buba ya ce, “Sojojinmu sun yi himma wajen kare ‘yan ƙasa da kuma rage barazanar ‘yan ta’adda a faɗin ƙasar.”
A yankin Kudu maso Kudu, sojoji sun lalata haramtattun matatun mai da kuma kama man fetur da aka sace.
Daraktan ya ƙara da cewar: “Yaƙi ba na sojoji ne kaɗai ba, na dukkanin ‘yan ƙasa ne. Muna buƙatar ƙarin goyon bayan al’umma don mu yi nasara a wannan yaƙi.”