✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun kashe ’yan bindiga 30 da suka kai wa sojoji hari a Abuja —DHQ

Dakarun sojin sun tabbatar da ci gaba da tsaron rayukan al'ummar kasar nan.

Hedikwatar Rundunar Tsaro ta Najeriya (DHQ), ta ce dakarunta sun kashe ’yan bindiga 30 daga suka kai wa sojoji hari a yankin Bwari da ke Abuja a ranar Lahadi.

Mai magana da yawun DHQ, Manjo-Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan ne a taron manema labarai kan ayyukan sojoji a Abuja.

Onyeuko ya ce dakarun rundunar tsaro ta 7 ne suka gudanar da aikin tare da rundunar sojin sama ta Whirl Punch daga Lahadi zuwa Talatar makon jiya.

Ya ce sojojin sun samu nasarar ce a kauyukan Kawu da Ido, inda suka kawar da ‘yan ta’adda tare da lalata matsugunansu da suke buya.

Kazalika, ya ce sojojin sun kwato babura shida da bindigogi kirar AK47 guda biyu.

“Shugaban rundunar sojin kasa da sauran hukumomin tsaro na sake tabbatar wa ‘yan Najeriya jajircewarsu wajen tabbatar da tsaro.

“Hare-haren kwanan nan da aka samu tsakanin ranar 23 ga Yuli, muna so mu tabbatar wa mazauna babban birnin kasar na Abuja cewa ba za mu gajiya ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.

“Ya kamata mutane su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.

“Muna neman goyon baya da hadin kan dukkan ‘yan Najeriya saboda lamarin tsaro aiki ne kowa.

“Ana bukatar ‘yan kasa da su kai rahoton duk wani wanda ba a saba gani ba a cikin al’umma ga hukumomin tsaro mafi kusa.

“Duk wani abu da aka gani kuma ba a yarda da shi a gaggauta sanar da mahukuntan da suka dace, ” in ji shi.

A nasa bangaren, Daraktan yada labarai rundunar tsaron kasa, Manjo-Janar Jimmy Akpor, ya bukaci kafafen yada labarai da su ci gaba da bai wa sojoji goyon baya wajen ganin an fatattaki makiyan kasar nan.