✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kashe N4.27bn kan harkar tsaro —Gwamnatin Katsina

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Inuwa ya ce jihar ta kashe Naira biliyan hudu da miliyan 270 daga watan Yunin shekarar 2015 zuwa Agustan…

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Inuwa ya ce jihar ta kashe Naira biliyan hudu da miliyan 270 daga watan Yunin shekarar 2015 zuwa Agustan 2020 a kan harkar tsaro.

Ya bayyana hakan ne a Katsina yayin da yake yi wa ’ya’a kungiyar ’Yan Jaridu ta Kasa (NUJ) jawabi ranar Litinin.

A watan Yulin da ya gabata ne wani dan kasuwa Alhaji Mahadi Hassan ya zargi Gwamnatin Jihar da kashe kimanin Naira biliyan 52 a kan harkar tsaro a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Sakataren ya ce gwamnati ta kashe kudaden ne karkashin ofishinsa wajen samar da kayan aiki da kuma biyan kudaden alawus din jami’an tsaro.

Ya ce sun kashe Naira 691 daga watan Yuni zuwa Disambar 2015; miliyan 827 daga Janairu zuwa Disambar 2016; miliyan 749 daga Janairu zuwa Disambar 2017 da kuma Naira miliyan 590 daga Janairu zuwa Disambar 2018.

Mustapha Inuwa ya kuma ce sun kashe Naira miliyan 682 a shekarar 2019, sai kuma Naira miliyan 732 daga Janairu zuwa Agustan 2020.

Ya ce gwamnatin jihar na kashe kudaden ne wajen karfafa gwiwar jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

“Gwamnatin Katsina tana daukar nauyin ayyukan jami’an tsaro tun daga rundunar tsaro ta Operation Sharar Daji na rundunar sojojin Najeriya shiyyar ta daya a jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara da Neja.

“Amma daga bisani kowace jiha ta dauki nauyin samar da ofisoshi da wuraren zaman jami’an da aka tura yankinta.

“Muna gyarawa, saye, dsa zuba mai ga motocin rundunonin tsaro na Operation Mesa, Operation Kan ka ce Kwabo, Operation Dirar Mikiya, Operation Sahel Sanity da dai sauransu”, inji Inuwa.