Rundunar sojojin Nijeriya ta ce an kashe masu ta da ƙayar baya 2245 a tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni na shekarar 2024, wato a tsukukun rubu’i na biyu na wannan shekarar.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Darektan kula da harkokin yaɗa labarai, Manjo-Janar Edward Buba ya kuma ce sojojin sun ƙwato makamai 2,783 da alburusai 64,547.
- ’Yan sanda sun kama masu ƙwacen waya 985 a Kaduna
- Shettima ya gana da gwamnoni kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata
Ya kuma bayyana cewa an kama aƙalla mutane 3,682 da ake zargi da aikata ta’addanci da sauran masu aikata laifuka yayin da aka kuɓutar da mutane 1,993 da aka yi garkuwa da su daga sansanin ’yan bindiga a samamen da suka kai daban-daban.
Manjo-Janar Buba ya kuma bayyana cewa, sojojin Nijeriya da ke aiki a ƙarƙashin rundunar “Operation Delta Safe”, sun gano cewa babu gaskiya dangane da rahoton da ke yaɗuwa na satar ɗanyen man fetur man da ya haura Naira biliyan 10.
Ya ce, “A cikin rubu’i na biyu na wannan shekara, sojoji sun kashe masu ta da ƙayar baya 2,245, sun kama mutane 3,682 da ake zargi da aikata ta’addanci da sauran masu aikata laifuka tare da kuɓutar da mutane 1,993 da aka yi garkuwa da su.
“Nasarar da muka samu a wannan lokacin ta haɗa da kwato lita 9,225,1489 ta ɗanyen man fetur da aka sace da lita 2,874,916 ta man dizel da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, da lita 29,900 ta kananzir da lita 31,380 ta man fetur da dai sauransu.”
A cewarsa, rundunar soji ta yi wa ‘yan tada ƙayar baya kaca-kaca sosai duk da cewa har yanzu suna nan suna gudanar ayyukansu.
Babban hafsan sojan ya ƙara da cewa, za a ɗauki lokaci wajen kawar da masu tayar da ƙayar bayan gaba ɗaya.