Shugaban kungiyar Tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa Kwamrade Umar danladi ya bayyana cewa sun kafa kungiyar ce domin su tallafawa gwamnatin wajen tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa.
Kwamrade danladi ya bayyana hakan ne a lokacin da suka kawo ziyara babban ofishin Aminiya da ke Abuja tare da daraktan harkar hada kan al’umma na kungiyar Ustaz Muhammad Auwal Abubakar Isa Abubakar.
“Idan aka yi ala’akari da rikice-rikicen da kasar nan ke fama da su irin na kabilanci da sauransu, wanda za ka ga ana kashe mutane da babu ruwansu, ana mayar da yara marayu, a mayar da mata zawarawa, kuma a yi asarar dukiya mai yawa. Ga kuma kalamam batanci. Kullum ana magana ne a kan hadin kan kasa, amma idan ana ci gaba da irirn wannan rikice-rikice, ba zai yiwu ba a cim ma gaci ba.
“ Kuma wannan abu ba gwamnati kadai yake damu ba, har da mu ‘yan kasa baki daya. Kuma babu kasar da ta ci gaba ba tare da zaman lafiya mai daurewa ba. Kuma zaman lafiya da kishin kasa kamar danjuma ne da danjummai. Dole a hadu su tare kafin a samu nasara. Wanna ne ya sa muka wannan kungiya domin mu taimaka wa gwamnatin wajen tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa.”
Da ya koma kan nasarorin da kungiyar ta samu kuwa, Kwamrade Umar cewa ya yi, “ Mun kafa wannan kungiyar a ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2016. Mun yi ayyuka da dama. Muna da bangarori da yawa kamar bangaren sasanta tsakanin addinai, akwai bangaren kiwon lafiya, inda muke kokarin wayar da kan al’umma a kan muhimmancin rigakafi da sauransu. Akwai kuma bangaren wayar da kan mata a kan muhimmanci zuwa awo, domin a samu kula mai kyau ga da da uwa. Kuma akwai bangaren maza ma inda muke wayar da kan maza a kan su bar mata su rika zuwa awo din. Kuma muna da bangaren wayar da kan al’ummma a kan muhimmacin mata su yi karatu. Da kuma ayyuykan gayya da muke shiryawa a gari sannan kuma muna da shiri na musamman a kan matasa a bangaren wayar da kan matasa musamman a kan illar shaye-shaye.
Da wakilinmu ya tambaye shi ko ina suke samun kudin da suke tafiyar da kungiyar, sai ya ce “Maganar kudi kuwa kasan komai bai yiwuwa sai da kudi. Mu tsakaninmu ne kawai muke tara kudi muke gudanar da ayyukan mu.
“Wannan ne matsalar da muke fusakanta a yanzu na rashin kayan aiki. Kasancewar kungiyar ba ta zama ba ce, muna yawo ne. Muna shiga kauyuka muna isar da sakonnin gwamnati a kan muhimmancin zama lafiya tare da hadin gwiwar sarakuna da hakimai. Don haka ne muke kira ga gwamnati da ta tallafa wa wannan kungiya da kudi da kayan aiki, kasancewar wannan kungiya mun kafa ta ne domin tallafa wa gwamnatin. Don haka muna kira ga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa mana. Kuma ina kira ga mutane da su san cewa samar zaman lafiya da aikin gwamnati bane kawai.”