A Jihar Zamfara, gwamnatin kan sayo babura cikin kwalaye a hada su, don ba da su bashi ga jama’a. Wannan lamari ya sa matasa da yawa suna samun abin yi, a wajen gudanar da wannan harka. Ganin yadda ake yawan samun bata-gari cikin harkar kanikanci, musamman ta babura, saboda kukan da wadanda ake ba su bashin baburan suke yi dangane da sace wadansu kayayyakin jikin baburan, ya sa kanikawan suka kafa kungiya. Sun bayyana cewa sun kafa kungiyar ce don su tsarkake sana’arsu. Wakilinmu ya tattauna da sakataren kungiyar, Malam Aminu Muhammad Gusau, don jin abubuwan da ta kunsa, kamar haka:
Aminiya: Malam Aminu, kai ne sakataren wannan kungiya, tun yaushe kuka kafa ta?
Sakatare: Mun kafa ta a shekarar 2012. Kuma mun yi haka ne ganin yadda abubuwa suka dagule cikin sana’armu. Muka nemi izinin uwar kungiyarmu ta kasa da ta jihar, suka yarda muka kafa ta.
Aminiya: Mece ce manufa?
Sakatare: Manufa ita ce don mu tsarkake sana’armu, ya kuma kasance mun san su wane ne ’ya’yanta. Abin da ke faruwa, yanzu sana’o’in hannu da yawa sun lalace, saboda za ka samu idan mutum yana kallon yadda ake yi masa aiki, shi ma kwana biyu, sai ya nemi kayan aiki ya ce ya iya. Da haka, sai ka ga ana ta samun matsaloli, ana ta zagin masu sana’ar, alhalin su ba su ne suka aikata laifin ba. To shi ya sa muka ga idan muka kafa kungiya, ko yaro za a yaye, sai an ba shi satifiket wato takardar shaidar ya iya. Wannan zai sanya ko ina ya tafi, zai iya bugun kirji ya ce lallai shi bakanike ne.
Aminiya: Wace hanya mutum zai bi don a dauke shi koyon sana’ar taku?
Sakatare: To na farko dai, dole sai mun dubi wanda ya tsaya masa, wato wanda ya kawo shi da inda za mu sahme shi. Kuma ka san harkar dukiya ce don haka sai an dauki mataki, ya kasance an san halayyarsa, wato tarbiyyar da yake da ita. Sannan za mu fada masa ko shekara nawa yaron zai yi, idan ya kammala, an sama masa ilimi, wanda zai iya dogara da kanshi, kuma zai iya daukar nauyin kanshi, sannan a ba shi dama, ya tafi ya bude wurinshi, a saya masa kayan aiki, ya tafi ya kama sana’a.
Aminiya: Wanda yake waje zai kalli wannan sana’a a matsayin wadda ba za ta iya daukar nauyin mutum da iyalinsa ba, yaya?
Sakatare: Wannan sana’a babu abin da ba za ta iya yi maka ba na rufin asiri. Matasan da suke da godiyar Allah, masu hakuri da kadan, sun sami arziki cikin wannan sana’a. Wasu sun sami muhalli; wasu sun sami motoci, sun yi iyali, sun sauke farali, sun yi makaranta, har digiri sun samu. To, me ya rage wa matashi idan ya sami wannan? Ka ga ke nan wannan sana’a ce mai tasiri kwarai da gaske. Abin da kawai ke damunmu shi ne rashin yi mata fandisho, har wasu ke kutsowa tun farko, shi ya sa wasu ke yi mata kallon banza, kamar ba ta da karfi, shi ya sa wasu ke kutsowa. Kuma wannan sana’a da ka ke gani, cikin wannan jihar ta fi kowace sana’a yawa da kuma mambobinta.
Aminiya: Yanzu kuna da mambobi nawa a kungiyar?
Sakatare: To a nan kawai muna da kanikawa wajen dubu hudu, kuma da muka zagaya sauran kananan hukumomi goma sha hudu, mun sami sama da dubu 25 a cikin jihar.
Aminiya: Ta yaya kuke samun kudaden shiga?
Sakatare: Ta hanyar dora wa kanmu haraji. Bambanci kawai shi ne idan memba ya ba da Naira ishirin ko dari biyu, shugaba zai ba da Naira dubu biyu ko biyar, don a kara a yi wani abu. Kuma muna taimaka wa su membobin. Misali akwai wanda ya karye, gwamnati ta dauke shi zuwa asibitin Kano, mu kuma sai muka rage masa nauyin iyalinsa. Banda wannan kuma idan wani ya sami matsalar bashi, misali, ko rigima har aka je kotu, mukan bi kadi, don magance wannan matsalar.
Aminiya: To yanzu mece ce babbar matsalarku?
Sakatare: To babbar matsalarmu ita ce za ka samu kungiyar ba ta kai tamu ba, amma suna samun wani tallafi daga gwamnati don su taimaka wa mutanensu, to amma da tsohuwar kungiya da mu, babu abin da muke samu, domin ko aikin hada mashina da ake daukar matasa kanikawa suna yi, ana daukarsu ne kan Naira 2,000, amma abin bakin ciki, sai wadanda aikin ke hannunsu su rika ba da shi kan Naira 500 kowane mashin daya. Gumurzun da za ka yi wajen hada shi ma, idan ka kwanta ko magani ba ka iya saya wa kanka. Wannan babbar matsala ce.