Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya ce sun gano ’yan bindgiar da suka sace daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya 39 da ke Afaka a Jihar Kaduna.
Sheikh Gumi ya shaida wa Aminiya cewa wasu shugabannin ’yan bindiga da ya hadu da su a daji a taron zaman lafiya da ya yi, sun taimaka wajen gano shugaban wadanda suka sace daliban, duk da cewa bai taba halartar taron zaman lafiyar ba.
- Yadda kayan hada rabobi ka sa kankancewar al’aura —Bincike
- Badala: Hisbah ta kama Daliban Jami’a a Kano
- An yi jana’izar tsohon Limamin Masallacin Harami, Sheikh Al-Sabuni
- ’Yan bindiga sun kashe mai gari a Sakkwato
“Mun gano shugaban da ya dauke daliban kuma bai taba halartar wani zaman lafiyar da muka yi a baya ba; Wadanda muka zauna da su sun gano shi.”
Mako biyu ke nan da daliban 39 ke hannun wadanda su yi garkuwa da su daga makarantar da ke hanyar zuwa filin jirgin sama a garin Kaduna, tun tun ranar Alhamis da dare.
Masu garkuwa da su na neman kudin fansa Naira miliyan 500, amma Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar ya yi fatali da batun yiwuwar tattaunawa da ’yan bindiga ko kuma biyan kudin fansa.
Sheikh Gumi ya ce duk da cewa an gano shugaban ’yan bindigar da suka sace daliban, umarnin Gwamnatin Tarayya na a harbe duk wanda aka gani dauke da bindiga kirar AK 47, ta sa bai samu ganawa da shi.
Malamin da gidauniyarsa sun sha tattaunawa da kungiyoyin ’yan bindiga a jihohin Zamfara, Neja da Kaduna a kokarinsa na shawo kansu su ajiye makamansu, kamar yadda yake neman Gwamnatin Tarayya ta yi musu afuwa.
Abin da ke kawo mana cika —Sheikh Gumi
Ya ce a tattaunawarsa da su a baya, ya gana da kusan kashi 80% na shugabannin ’yan bindiga.
A cewarsa, rashin samun kwarin gwiwa daga wasu jami’an gwamnati ne da ya sa bai samu ganawa da dukkansu, ya shawo kansu su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya ba.
“Da mun samu goyon baya, da mun gana da dukkansu. Duk wadanda muka gana da su sun yarda su taimaka wurin tattaunawa a madadinmu kamar yadda ake yi a Jihar Neja idan aka sace mutane.
Dalilin rashin zamanmu da su
“Yanzu mun kai matsayin da muke iya gano wadanda ke da hannu a miyagun ayyuka.
“Mun gano shugaban da ya dauke daliban kuma bai taba halartar wani zaman lafiyar da muka yi a baya ba.
“Wadanda muka zauna da su sun gano shi, amma ba mu samu yin zama da shi ba saboda hatsarin da ke tattare da hakan, kasancewar gwamnati ta ba da umarnin a harbe su a duk inda aka gan su kuma ta ce ba za ta tattauna da su ba.
“Saboda haka ne ba na son mu shiga cikin daji, gwamnati ta dauka cewa muna ba su kwarin gwiwa ne.”
Yadda za a ceto daliban
Game da yadda za a ga cewa an sako daliban, Gumi ya ce, “Abin da nake gani shi ne gwamnati ta dan saurara ta bari mu shiga mu koyar da su yadda za su gudanar da rayuwa, mu yi musu nasiha sannan a yi sulhu da su domin sun daina.
“Wannan abu kanmu muke yi wa, ba wata gwamnati ko wata jam’iyyar siyasa ba.
“Ba ma so a bar ’yan siyasa su dagula al’amura, su zuwa suke yi su hau mulki su sauka bayan dan lokaci, mu kuma muna nan da yardar Allah.
“Mu ba don siyasa muke yi ba, kanmu muke yi wa domin mu ga an kawo karshen zubar da jinin mutane,” inji shi.
‘Ba zan canza wa El-Rufai ra’ayi ba’
Game da matsayin da El-Rufai na kin tattaunawa da ’yan bindiga, Sheik Gumi ya ce, “Ba zan iya canza wa gwamnatin jihar matsayin da ta dauka kan tattaunawa da su ko biyan kudin fansa ba.
“Abin da kawai nake so daga gareta shi ne ta bari mu ci gaba da tattaunawa da su ’yan bindigar,” a cewarsa.
Kokarin da muka yi don jin ta bakin Gwamnatin Jihar Kaduna ta hannun Kwamishinan Tsaron da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya ci tura saboda kiran wayarsa ba a amsa ba.