Gwamnan Jihar Abiya, Alex Otti, ya ce sun gano gawarwaki 80 a wata maboyar masu garkuwa da mutane da ke Jihar.
Ya kuma ce bayanan sirrin da jami’an tsaro suka tattara ya gano cewa kusan dukkan kudaden fansar da masu garkuwa suka karba a kan kai su ne kusa da kasuwar shanu ta Umuchieze da ke Karamar Hukumar Lokpanta a Jihar.
- Ana harbe-harbe a Ribas bayan majalisar Jihar ta fara shirin tsige Gwama
- Kudaden aikin da ake ba ’yan majalisa sun yi kaɗan – NILDS
Gwamna Alex ya ce sun sami nasarar gano hakan ne bayan sun karkafa wasu na’urorin zamani a sassan Jihar daban-daban.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman ta wata-wata da yake yi da ’yan jarida a gidan gwamnatin Jihar da ke Umuahia, babban birnin Jihar.
Ya ce, “Mun kafa wadannan na’urorin ne domin gano abubuwan da suke faruwa a lungu da sako ma jiharmu.
“Yan makonnin da suka gabata, mun gano cewa da yawa daga kudaden fansar da masu garkuwa da mutane suka karba an kai su wani waje ne da ke Karamar Hukumar Umunneochi.
“Hakan ce ta sa muka yanke shawarar yi wa wajen tsinke, kuma abin da muka gano ya daure mana kai. A cikin kasa da sa’o’i 48, mun gano gawarwaki 80 a kusa da kasuwar shanun, sannan mum gano gawarwaki 20 babu kawuna har sun fara rubewa, ciki har da na manya da yara.
“Mun kuma gano ƙwarangwal ɗin mutane da aka kashe sannan aka bar su har suka rube suka zagwanye a dai yankin,” in ii Gwamnan.