✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun gaji da gafara sa kan matsalar tsaro – Malaman Kaduna ga Buhari

Majalisar malaman da limamai ta ce alhakin rayukan wanda suka mutu na kan gwamnati

Majalisar Limamai da Malamai ta Jihar Kaduna ta ce sun gaji da gafara sa kan matsalar tsaro, inda suka bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya dauki mataki kan harin bam din da ’yan ta’adda suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Majalisar ta ce dole ne a dora wa gwamnati alhakin duk wani rai da aka rasa a sanadin harin.

A wata sanarwa da Babban Sakataren majalisar, Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, ya fitar a ranar Laraba, ya ce akwai bukatar daukar mataki ba wai yin surutu kawai ba.

Yayin da ya ke jajanta wa ’yan Najeriya game da harin, ya bukaci gwamnati da ta tabbatar da tsaro ga ’yan kasa.

Sanarwar ta kara da cewa, “Majalisa ta kalubalanci yadda gwamnatin Najeriya ke yaki da ’yan bindiga; mun yi imanin cewa yadda ake yakarsu ba zai samar da sakamakon da ake bukata ba.

“Jami’an tsaron Najeriya sun san maboyar ’yan bindigar nan sarai, amma duk da haka ’yan bindigar suna aiwatar da ayyukansu ba tare da wata fargaba ba. Ya isa haka da irin halin ko in kula da rayukan al’umma da gwamnatin Najeriya ke yi.

“Dole ne a dora wa gwamnati alhakin duk wani rai da aka rasa. Muna bukatar gwamnati da ta tabbatar da tsaro a kauyukanmu da hanyoyinmu tare da tabbatar da cewa muna cikin koshin lafiya, ya isa haka Shugaban Kasa, muna bukatar ka dauki matakin da ya dace,” inji majalisar.