Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta sanar da shirinta na hada kai da kungiyar ’yan bori, wadanda aka fi sani da masu aiki da aljanu.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce hukumar za ta yi aiki da ’yan borin ne da zimmar tsaftace ayyukansu ta yadda za su yi daidai da doka.
Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a safiyar Talata ta ruwaito cewa Abba El-Mustapha ya sanar da haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ’yan bori reshen Jihar Kano a ofishinsa.
El-mustapha ya nemi hadin kai tare da cikakken kungiyar ’yan borin ta yadda a cewarsa, za a gudu tare a tsira tare.
A jawabinsa amadadin kungiyar, shugaban majalisar ’yan bori masu aiki da aljanu na karamar Hukumar kumbotso, Mal. Sabo isyaku wailari, cewa ya yi sun ziyarci hukumar ce domin kulla alaka ta bangaren da aikinsu ya hadu.
A cewarsa, bangaren ya hada da tallata maganin gargajiya domin su tabbatar da ’ya’yan kungiyar suna amfani da kalmomin da ba su saba dokokin hukumar ba.
Ya kara da cewa kungiyar tana yin iya kokarinta wajen tabbatar da cewa mambobinta ba su yin wasa a lokacin daya ci karo da lokacin sallah ba, ko a kusa da masallatai, makabartu ko makarantu.
A karshe ya yi wa hukumar alkawarin cewa kungiyarsu za ta ci gaba da ba wa hukumar cikakken hadin kai tare da goyan baya.