Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da daƙile wani yunƙurin hamɓararren Shugaban ƙasar Mohamed Bazoum na tserewa tare da iyalinsa.
Kakakin gwamnatin sojin Nijar, Kanar-Manjo Amadou Abdramane, wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya yi wa jama’ar ƙasar ta Talabijin, ya ce Bazoum da iyalinsa sun tsara guduwa daga Fadar Shugaban ƙasar ne da misalin ƙarfe uku na dare.
- Martanin tubabbun ’yan Boko Haram kan tuban muzuru
- Kamfanin Nokia zai sallami ma’aikata 14,000 saboda rashin ciniki
Ya ce Mohamed Bazoum ya yi kokarin tserewa da karfe 3 na safiyar ranar Alhamis tare da iyalansa masu dafa masu abinci 2 da kuma jami’an tsaro guda biyu.
Sai dai a cewar sojojin, wannan yunƙurin da bai kai ga ci ba, na cikin wani tsari da aka shirya da kuma sojojin suka ce suke bi sau da kafa.
Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce “matakin farko na wannan shiri shi ne na su fice daga cikin fadar zuwa kewayen wurin inda wata mota ke jiransu daga nan ne za a dauke su zuwa wani gida da ke cikin unguwar Tchangarey.
“Sannan daga nan kuma a nufi wani wuri inda wasu jirage biyu masu saukar ungulu na wata kasa da sanarwar ba ta bayyana ba za su kai su Birnin Kebbi da ke Najeriya.’’
Sanarwar sojojin ta kuma jinjina wa sojojin da hazakarsu da kuma himmar su ta ba da damar dakile wannan yunkurin tare da kare rayuka.
Ana tsare da Bazoum da matarsa da kuma ɗansa ne tun bayan da sojoji suka yi wa gwamnatinsa juyin mulki a cikin watan Yuli.
Tun bayan juyin mulkin ne aka raba gari tsakanin kasar ta Nijar da uwargijiyarta Faransa ta hanyar korar jakadanta da kuma sojojinta 1500 da ke yaki da kungiyoyin masu da’awar jihadi a yankin Sahel musaman a yankin iyakoki 3.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 24 ga watan Satumba Shugaba Emmanuel Macron ya ce Faransa za ta kwashe dukkan dakarunta da jakadanta da ke Nijar nan da karshen shekarar 2023.
Wannan na zuwa ne bayan Jakada Sylvain Itte ya fice daga kasar wata guda bayan sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum sun ba shi wa’adin awa 48 ya bar kasar bayan “ya ki amsa gayyatar ma’aikatar harkokin waje don halartar taron” da aka gayyace shi da kuma “wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar.”
Nijar dai na daya daga cikin kawayen kasashen yammacin duniya a yankin Sahel da suke yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai masu alaka da Al-Qaeda da IS.
A kan haka ne kungiyoyin yammacin Afrika irin su ECOWAS da UEMOA suka kakabawa kasar takunkumi domin tilastawa sojojin mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.