Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola, ya ce sun cika da mamakin yadda dan wasan gaba na kungiyar Erling Haaland ke zura kwallo.
Guardiola ya ce sun cika da mamaki musamman yadda Haaland ya kafa tarihin zura kwallo a kakar wasan sa ta farko a City kuma a Ingila.
- PSG ta dauki matakin ladabtar da Messi kan kai ziyara Saudiyya
- Jirage sun kai hari kan fadar Shugaban Kasar Rasha
Kawo yanzu a wannan kakar dai, Haaland ya zura kwallon sa ta 50 a City a karawar da suka yi da Fulham.
Dan wasan na Norway a yanzu na kokarin kafa tarihin yawan zura kwallo a gasar Firimiyar Ingila a kaka guda, ganin yadda ya taddo yawan kwallaye 34 da ‘yan wasa Alan Shearer da kuma Andrew Cole suka ci a gasar.
A zantawar da Guardiola ya yi da manema labarai gabanin wasan su da West Ham United a Laraban nan, ya ce abinda Haaland ya yi ya basu mamaki amma kuma kila shi baiji mamakin abinda ya yi ba ganin ya taba yin hakan a wasu gasanni da ya fafata.
Ya ce suna fatan dan wasan zai ci gaba da nuna bajinta wajen zura kwallo daga yanzu har zuwa karshen kakar wasan bana.