Wasu daliban makarantar Noble Heigts College, da ke Karu, a Abuja, sun yi hobbasa inda suka bude wani dan karamin kamfani, inda suke hada abubuwan da suka shafi abinci, da sauran kayan tande-tande.
Baya ga bude kamfanin, wadannan daliban sun samu nasarar lashe gasar kamfanoni na shekara ta Najeriya, wanda ya wakana a Jihar Legas, kuma yanzu za su tafi kasar Afirka ta Kudu inda za su wakilci Najeriya a gasar ta Afirka.
daliban, Olumide Adeleke wanda ke da burin zama likitan canja gabban jiki, wanda shi ne shugaban kamfanin, sai Sadiya Mukhtar mai son zama likita, wadda ita ce mataimakiyar shugaba na bangaren kudi, sai Yaduna Debine Susuti, mataimakiyar shugaba bangaren aikace-aikace, da kuma Etokudo Eebents Blessing, su ne wadanda za su tafi kasar Afirka ta Kudu, domin wakiltar Najeriya.
Malamin da ke kula da lamarin kamfani mai suna Mista Lucky Daniel Idehen, ya shaida wa Aminiya cewa sun bude kamfanin ne domin su koyar da daliban sana’o’i, domin su yi dogaro da kansu bayan sun kammala makaranta. Sannan kuma ya tabbatar da cewa daliban sun samu ilimin sana’o’in ta yadda ba ya shakkar ko bayan sun kammala karatu, ko ina suka je za su nuna kwarewa. “Ko sun bar makarantar nan, duk inda suka je, za su yi amfani da sana’ar da suka koya.”
Kamfanin Flourishers, suna hada abinci daban daban da suka hada da wani nau’in abin kari mai suna breakfast granola, da unripe plantain flour, da been flour da sauransu. Suna da mahukunta 11, da mutum 30 masu zuba jari.
Shugaban kamfanin, Olumide ya nuna cewa kayan kamfaninsu na da karko da aminci matuka, “Abin da ya sa kayanmu ya zama daban da na sauran shi ne muna lura da aminci matuka. Ko ledar da muke saka kayanmu a ciki mai kyau ne. kuma za a iya budewa a saka rufewa. Wanda hakan ya sa kayan ke iya dadewa, kuma yana da kyau kamar yadda aka sayo,” inji Olumide.
Da farko kamfanin ya fara ne da neman jarin da za su fara aiki, a cewarsu “Mun fara da ne jarin Naira dubu 98, wanda muka tara bayan mun sayar da ice cream da hot dogs, sai kuma muka sayar da hannun jari ga iyaye da malaman makarantarmu.
“Daga nan sai muka samu ribar kudi Naira dubu 332,700. Wanda muka yi amfani da kashi 20 na kudin wajen taimakon al’umma na kusa da mu a matsayin tallafin da kamfani ke fitar wa. Sannan muka raba kashi 45 a matsayin riba ga wadanda suka zuba jari, sannan kuma kashi 30 muka biya albashin ma’aikata.
Sun kara da cewa sun yi fama da matsaloli musamman wajen tara jarin da za su fara aiki, “An dade ana irin wannan tsarin a wannan makaranta, mu kan sayar da hannu jari domin mu samu kudi, amma sai ya kasance wasu lokuta da suka wuce ba a samu riba mai kauri, wanda hakan ya sa aka samu matsaloli, har wadansu mutane suke ganin cewa akwai matsala a tafiyar,” inji shugaban kamfanin.
“Saboda wannan ne sai da muka sha wahalar gaske wajen gamsar da mutane cewa wannan karon akwai nasara, domin mun shirya sosai. Da kyar muka samu suka amince da mu. Kuma cikin ikon Allah, a karon farko, mun samu riba mai kauri, kuma mun ba kowa abin da ya samu,” inji Mista Lucky.
Kamfanin ya shirya tsaf a yanzu haka domin ya wakilci Najeriya a gasar kamfanoni na Afirka a kasar Afirka ta Kudu “Mun fara da shiga gasa a nan Abuja, inda muka samu nasara, sai muka shiga na yankin Arewacin Najeriya, nan ma muka yi nasara, sai kuma muka wakilci Arewa a gasar ta kasa baki daya a Jihar Legas, nan muka samu nasarar lashe gasar.
“Yanzu haka mu ne za mu wakilci Najeriya a gasar ta Afirka ta Kudu a ranar 5 ga watan Disamba mai zuwa, inda kasashe 11 za su zo mu fafata, kuma ko shakka babu, muna sa ran cewa za mu lashe gasar.”
Baya ga wadannan nasarori da muka samu, mu ma mun tallafa wa mutanen da suke kusa da mu, ta hanyar tallafawa mabukata da kayan abinci, da kaya da sauransu. Kuma mun koya ma wasu yadda muke hada kayan kafaninmu ta yadda za su yi dogaro da kansu, kuma mu rage rashin aikin yi. Sannan kuma mun dauki nauyin dalibai guda biyu a Firamaren makarantarmu duk da ribar da muke samu.