Rahotanni na bayyana cewa, an samu mummunan hadarin motoci biyu na karamar motar shiga kirar Audi da kuma kirar Toyota Camry wanda ya sanadiyyar rasuwar mutum biyar nan take.
A cewar wani ganau ya ce, hadarin ya faru ne da misalin karfe 2 na tsakar daren yau Laraba a hanyar Marian kafin iyakar Atekong a Kalaba babban birnin jihar Kuros Riba.
Bayan aukuwar hadarin Jami’an ‘yan sandan sun kwashe motocin da suka yi hadarin da gawarwakin mutanen.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kiyaye hadura ta Najeriya FRSC na jihar Godsgift Uwem ya tabbatar aukuwar lamarin.