Tsohon manemin takarar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Jibrin Dan Barde, ya bayyana cewa mulkin ’yan uwa da abokai ake yi ba mulkin siyasa ba a karkashin jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar.
Jibrin Dan Barde, wanda ya zo na biyu yayin zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC a zaben 2019, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP a sakatariyar jam’iyyar da ke Jihar.
- Kamfanonin sadarwa sun yi asarar masu amfani da data miliyan 1.27
- Jerin sunayen iyalan Sarkin Kajuru da ke hannun ’yan bindiga
A nan ne ya tabbatar da zamansa dan jam’iyyar PDP wanda yake son ya yi mata takarar gwamna a shekarar 2023 bayan ya mallaki katin jam’iyyar tun a ranar 2 ga watan Fabarairu.
Ya ce mulkin da ake yi Gombe kowa ya shaida ba mulkin demokuradiyya bane don ba wanda yake jin dadin gwamnatin.
Dan Barde, ya ce a 2023 jam’iyyar PDP ce za ta kafa gwamnati a Gombe kuma jama’a za su ga yadda ake mulkin siyasa ba ta dangi ba.
“Masarautun mu abun alfaharin mu ne da muke mutuntawa ya za a yi tun farko ka ci mutuncin sarakuna yanzu kazo ka kara musu albashi,” inji Dan Barde.
A nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Gombe, Janar Abna Kwaskebe, ya ce suna maraba da dawowar Dan Barde jam’iyyar PDP kasancewarta jam’iyyar ce mai son jama’a.
Kwaskebe, ya ce a baya sunyi kuskure wanda shi ya janyo musu faduwa a zabe amma yanzu sun gyara kuma za su karbi mulki a 2023.
Ya ce suna da abun nuna wa jama’a da jam’iyyar su tayi wanda zai basu damar cin zabe cikin sauki.
Daga karshe ya ce basu gamsu da mulkin APC ba daga sama har kasa don haka suke sukar ta don basu ga abin da ta aika ta ba.
A bangaren jam’iyya mai mulki ta APC, da Aminiya ta tuntubi shugaban jam’iyyar ta wayar salula, Mista Nitte K Amangal ya ce suna wani taro idan suka gama zai waiwayi wakilinmu amma har zuwa lokacin tattara wannan rahoto bai kira ba.
Hakazalika, shi ma Jami’in Hulda da Jama’a na jam’iyyar da aka tuntuba bai amsa kiran wayarsa sannan bai bayar da amsar sakon kar-ta-kwana da aka aike amsa ba.