Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta Jihar Gombe (GOSEPA) ta sanar da sababbin matakan ladabtarwa masu tsauri ga masu karya dokar tsaftar gari na ƙarshe wata.
Ciki har da tara mai tsanani da tura masu laifi gidan gyaran hali.
- Mun ceto yaran Kebbi 19 da aka yi safararsu zuwa Calabar – NAPTIP
- Za a hukunta iyayen da suka hana yara samun ilimi a Adamawa
Babban Sakataren Hukumar GOSEPA, Dokta Auwal Baba Jada, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai, inda ya ce daga ranar Asabar 25 ga Janairu, za a fara aiwatar da wannan doka tare da tallafin kotun tafi da gidanka.
“Matakin ya zama dole saboda rashin bin dokar tsaftar ƙarshen wata da ake gudanarwa a jihar. Duk wanda aka kama yana karya doka bayan kammala tsaftar muhalli zai biya tara, kuma idan ya ƙi biya za a tura shi gidan gyaran hali,” cewar Baba Jada
Ya ce, tarar da za ta fuskanci masu sana’ar Akori-Kura da suke ɗiban yashi da masu tankar ruwa, Naira dubu 20 masu babura, Naira 5,000, masu shaguna da gidajen mai Naira 200,000.
Baba Jada ya ce, “Wannan matakin ya zama dole saboda al’ummar jihar ba sa kula da dokar tsafta da ke tilasta zama a gida na tsawon sa’o’i uku don tsaftace muhalli. A wannan karon, duk wanda ya karya dokar zai fuskanci hukunci mai tsanani.”
Ya ƙara da cewa, masu zuwa filin wasa (stadium) suma sun shiga dokar. “Dole su gama ayyukansu kafin ƙarfe bakwai na safe ko su jira har bayan ƙarfe goma na safe. Muddin suka fito cikin lokacin dokar, za a kama su,” in ji Baba Jada.
Dokar ba ta shafi ma’aikatan jin ƙai, jami’an kwana-kwana, ma’aikatan lafiya, ‘yan jarida, ma’aikatan ruwa da ma’aikatan wutar lantarki NEPA, amma sai da ƙwaƙƙwaran dalili.