Tsohon Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Obi/Datti, Mista Doyin Okupe ya ce an kulla alkawari cewa yankin Arewa zai mulki Nijeriya tsawon shekara takwas sannan yankin Kudu ya karba na tsawon shekara takwas.
Doyin Okupe ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga yankin Arewa ya yi shekara takwas a bisa mulki, don haka Tinubu da ke kan mulki zai yi shekara takwas idan yana so.
Okupe wanda tsohon kakakin tsohon shagaban kasa Goodluck Jonathan ne, ya ce Tinubu na iya cin zaben shugaban kasa a 2027 idan ya iya shawo kan matsalolin da ke damun Nijeriya a yanzu.
A yayin da ake hira da shi a shirin siyasan gidan talabijin na Channels, Okue ya ce, “Tinubu na yin abin da ayaba soja kuma nan gaba zai yi abin da ya fi hakan. Abin da yake bukata shi ne a kara fahimtarsa ba yi masa zagon kasa ba.
- Kotu ta sallami kananan yara da ake zargi da cin amanar kasa
- Malaman addini na yaudarar mabiyansu saboda abin duniya — Sarkin Musulmi
“Idan ba a shiga wannan mawuyacin halin ba, watakila da kasar nan ta durkushe, kuma na yi imanin idan aka ba shi karin lokaci zai gyara kasar nan.
“‘Yan Nijeriya ne za su yi alkalanci, kuma na tabbata san sun abin da ya kamata, kuma ba su takura wa shugabanni ba. Idan Tinubu ya magance matsalar man fetur da tsadar abinci kafin lokacin, mutane za su ce idan ba shi ba sai rijiya.
“Bola Tinubu ba sakarai ba ne, ya san idan bai yi hakan da kyau ba daga yanzu zuaw 2027 ba zai kara samun wata dama ba. A kasar nan an yi alkawari cewa yankin Arewa zai yi shugabanci na shekara takwas sannan yankin Kudu ya yi takwas.
“Buhari bai tabuka abin kwarai ba amma duk da haka ba mu haukace masa ba. Amma Tinubu na yin abin da ya dace, don haka zai yi shekara takwas idan Allah Ya ba shi tsawon kwanan kuma ya so.”