Babu abin da mulkin Atiku Abubakar zai haifar a Najeriya illa hargitse da kawo rarrabuwar kan ‘yan kasa idan har aka zabe shi a 2023, a cewar jam’iyyar APC.
Jam’iyyyar ta fadi hakan ne a matsayin martani ga kalaman dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a jawabinsa a wani taron bayyana manufofi da aka gudanar a Gidan Arewa da ke Jihar Kaduna a ranar Asabar.
- Tinubu ya ziyarci Sarkin Zazzau bayan tafiyar Atiku
- Rikicin cikin gida ya hana PDP samun dan takarar Gwamnan Ogun a 2023
Jam’iyyar APC ta fadi haka ne a cikin wata sanarwa wacce Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Barista Felix Morka ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar na cewa, wadannan kalamai ba su kamaci tsohon Mataimakon Shubagan Kasa ba, don haka mutane su yi watsi da shi a babban zaben mai zuwa, su zabi nagarta da sanin ya kamata a Tinubu.
A wani bidiyo da ya karade dandalan sada zumunta, an jiwo Atiku na cewa “Babu wanda ’yan Arewa suke so ya jagorance su face dan Arewa kuma ba Bayarabe ba kuma ba dan kabilar Ibo ba.”
Wannan furuci ya sanya mutane ke ta tofa albarkacin bakinsu da ta kai ga Jam’iyyar APC ta fito ta yi tir da kalaman nasa, inda ta tallata nata dan takararta, Asiwaju Bola Tinubu a matsayin shi ne wanda ya fi cancanta a zaba a 2023.