✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mukarraban El-Rufai sun kamu da COVID-19

Makusantan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ciki har da iyalai da kwamishinoni sun harbu da cutar COVID-19. Yanzu haka ana jinyar manyan jami’an Gwamnatin El-Rufai…

Makusantan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ciki har da iyalai da kwamishinoni sun harbu da cutar COVID-19.

Yanzu haka ana jinyar manyan jami’an Gwamnatin El-Rufai da suka kamu da cutar kwana hudu bayan El-Rufai ya sake killace kansa a karo na biyu.

“Ma’aikata da dama, Kwamishinoni da sauransu da muke aiki tare a kowane lokaci sun kamu da cutar.

“Na yi tafiya na dan lokaci, amma bayan da na dawo mun yi aiki tare da wasu daga cikin mutanen da yanzu suke a killace,” inji shi.

El-Rufai, a hirarsa da kafafen yada labarai da ke Kaduna ranar Laraba da dare, ya ce yanzu haka ana jiran sakamakon gwajin cutar da aka yi wa wasu jami’an gwamnatinsa.

Ya ce: “Ba zan ambaci suna ba amma yawancinsu manyan jami’an gwamnati ne; wasu na jiran sakamakon gwajin da aka yi musu wasu kuma sun kamu da cutar.”

Sai dai ya ce ya samu nustuwa bayan sakamakon da aka kawo na gwajin da aka yi masa ranar Lahadi ya nuna ba ya dauke da kwayar cutar.

A ranar Larabar ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta rufe kafatanin makarantun da ke jihar.