✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai da Majalisar Kaduna: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 17 ga Yuli

El-Rufai ya ƙalubalanci rahoton Majalisar Dokokin Kaduna, kan zarginsa da cin hanci da rashawa.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kaduna, ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya shigar da Majalisar Dokokin jihar da kuma Babban Lauyan jihar.

El-Rufai yana ƙalubalantar rahoton kwamitin majalisar, wanda ya zarge shi da cin hanci da rashawa da karkatar da dukiyar al’umma jihar.

A lokacin da aka fara sauraron karar a ranar Litinin, lauya mai kare wanda ake ƙara, Sani Katu (SAN), ya sanar da kotu cewa suna kan shirye-shiryen gabatar da takardar ƙin amincewa da ikon kotun na sauraron shari’ar.

Don haka lauyan ya buƙaci a ƙara lokaci don ba su damar shigar da duk aikace-aikacensu kan ƙarar El-Rufai ya shigar.

Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin jihar, Sule Shauaibu (SAN), na cikin waɗanda ake tuhuma a ƙarar.

Lauyan da ya shigar da ƙara, Sule Umoru, bai yi watsi da rokon ƙarin lokaci ba.

Bayan sauraron duk hujjojin lauyoyi, mai shari’a Rilwan M. Aikawa, ya ɗage shari’ar zuwa 17 ga Yuli, 2024, don ba wa waɗanda ake ƙara damar gabatar da dukkanin takardunsu.

Idan za a tuna cewa a ranar 26 ga Yuni, 2024, El-Rufai ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya ta Kaduna, don ƙalubalantar rahoton binciken da Majalisar Dokokin Jihar ta gabatar, wanda ya zarge shi da cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa na tsawon shekara takwas.

Ya nemi kotu ta soke rahoton majalisar, saboda a cewarsa ya tauye wasu haƙƙoƙinsa da kundin tsarin mulki ya tanada.

Ya ce ba a gayyace shi don kare kansa daga zarge-zargen da ake ba.