✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Mukamin Minista ne ya dace da Peter Obi ba Shugaban Kasa ba’

Ya ce Peter Obi ba shi da abubuwan da ake bukata na zama Shugaban Kasa

Tsohon dan Majalisar Wakilai, Ned Nwoko, ya ce dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi zai fi dacewa da Ministan Tattalin Arziki amma ba Shugaban Kasa ba.

Nwoko a wata tattaunawa da BBC a ranar Talata ya ce Peter ba shi da abin da ake bukata a shugabancin kasa, amma yana da sani a fagen kasuwanci.

Ya ce, “Peter Obi mutumin kirki ne kuma yana burge ni. Lokacin da ya zo birnin Landan shi kadai ya zo. Dan jari hujja ne da ya jima ana damawa da shi a duniyar kasuwanci, kuma mai ra’ayin ’yan mazan jiya.

“Zan so ya dawo jam’iyarmu ta PDP don zai yi kyau da Ministan Tattalin Arziki, wanda zai taimaka mana mu farfado da kasar daga mawuyacin halin da take ciki,” inji Nwoko.

Kazalika tsohon dan Majalisar ya ce akwai matsalolin da za su hana shi samun shugabancin kasar musamman saboda ba shi da wasu abubuwan da ake bukata.

“A matsayin shugaban kasa yana bukatar ’yan majalisa daga jam’iyyarsa su sami rinjaye a majalisa, abin da mawuyaci ne ya samu,” inji Nwoko.