Shekara biyar bayan ta yi batancin ga Manzon Allah (SAW) a shekarar 2015, Mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta sake wallafa zanen barkwanci da sunan siffanta Manzon Allah (SAW).
Charlie Hebdo wadda ta shahara wurin zanen barkwanci ta wallafa zanen ne kwana a jajibirin shari’ar mutane 4 da ake zargi da taimakon wasu mahara biyu masu da’awar jihadi da kai harin bindida a ofishinta a 2015 bayan ta wallafa zanen batancin.
Charlie Hebdo wallafa wasu zanen barkwanci na batancin har guda 12 a shafinta na farko, bayan da farko wata wata jarida ta harshen Danish na kasar Denmark ta fara wallafa su a babban shafinta.
Harin da aka kai wa Charlie Hebdo bayan kasassabar ta 2015 ya yi ajalin mutum 12 a ofishinta, ciki har da wasu fitattun masu zanen barkwanci; baya ga wasu mutum biyar da aka kashe daga baya a birnin Paris.
Ana ganin harin da aka kai wa mujallar a 2015 su ne tushen hare-haren masu ikirarin jihadi a kasar Faransa.
Cikin batancin da mujallar ta yi har da zane da ta yin a nuna wani butumbutumi sanye da bam a kansa.
Mujallar na ikirarin cewa tun bayan da ya faru a 2015 take samun kiraye-kiraye neman ta ci gaba da zane-zanen barkwanci.
Ta ce, “Mun ki yin hakan ne ba wai don za a hana ba amma kafin mu yi muna neman dalili mai ma’ana da zai kawo muhawara.
“Sake wallafa zanen barkwancin a makon da ake yin shari’ar wadanda suka kai hare-haren 2015 na da muhimmanci a gare mu”, inji ta.
Tun dai kamar yadda aka yi a baya, al’ummar Musulmi daga sassan duniya suka dukufa la’antar wannan cin mutunci da mujallar ta yi wa Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).
Shari’ar Musulunci ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi batanci ga Manzon Allah, sai dai kasar Faransa na daga kasashen da da’awar duniyanci, tare da dokoki da ake ganin sun kuntata wa addinin Musulunci da Musulmai.