Idan masu karatun wannan shafi na biye da mu, a makon da ya gabata ne muka tabo bangaren maza inda suke korafin rashin samun wadatuwar zuci a game da yadda suke samun biyan bukatar kwanciyar aure daga matansu. Mun ji yadda wadansu magidanta suka yi korafi a game da yadda matansu suke azabtar da su idan bukatar kwanciyar aure ta taso. Mun kuma ji irin shawarwarin da muka bayar ga matan da suke nuna irin wannan mugun hali. Da fatan irin wadannan matan za su ji kuma za su amfana daga abin da muka kawo.
To a yau, kamar yadda na yi alkawari zan karkata akalar ce ga bangaren maza, yadda suke cutar da matansu a game da karancin kwanciyar aure (ibadar aure). Kamar yadda muka sani ne, jigo ko ginshikin aure dai shi ne kwanciyar aure. Don ta kwanciyar aure ne ake samun zuri’a. Babban burin kowane ma’aurata shi ne su yi aure kuma su hayayyafa kamar yadda su ma iyayensu suka haife su. Saboda haka karancin samun ibadar aure daga mata da miji ba karamar illa ba ce.
Don haka ga wadansu matsalolin da mata ke fuskanta daga wajen mazaje a bangaren kwanciyar aure.
Idan mace ta auri namijin da bai iya biya mata bukata a kwanciyar aure, akwai matsala. Za ka tarar wadansu mazajen saboda wadansu dalilai na kashin kansu ba kasafai suke son biya wa matansu bukata a wajen kwanciyar aure ba. Daga cikin irin wadannan dalilai da ke kawo haka, kamar yadda wadansu mazaje suka shaida mini akwai na kiyayya. Abin da nake nufi da kiyayya a nan shi ne, watakila tun da farko mijin ba ya son matar amma aka tilasta masa ya aure ta, to wannan kiyayya tana yin tasiri a wajen yadda yake kula matar da kuma yadda yake kwanciyar aure da ita.
Mafi yawan mazajen da ake musu auren dole za ka tarar ba kasafai suke kusantar matan da aka daura musu aure da su ba, don ko da ma sun kusance su, to ba sa jin dadin biyan bukatar aure da irin wadannan mata. Saboda haka ya dace iyaye su rika la’akari da irin auren da suke hadawa a tsakanin mata da miji. Yana da kyau a rika samun amincewa da kuma soyayyar juna kafin a yi aure don hakan yana da matukar tasiri a rayuwar zamantakewar aure. Kuma haka abin yake a bangaren wadansu mata idan ba ta son namiji, to ba kasafai suke amincewa su rika yin kwanciya aure da shi ba. Ko da ma sun yarda za ka tarar babu armashi don suna yin haka ne tamkar a kan dole.
Amma a wasu lokutan kuma laifin na mazan ne, wadansu mazan saboda yadda suke neman matan banza a waje, idan suka koma gida ba kasafai suke kusantar matansu na sunna ba. Kamar mai jin yunwa ne, da zarar ka ba shi abinci ya cika cikinsa, to idan ya je wani waje aka sake ba shi abinci, ai da wuya ne ya iya ci, saboda ya koshi. To irin wadannan mazaje hakan ke sa suke kauracewa matansu na gida, don su a wajensu sun riga sun biya bukatarsu a waje. Wannan kuma cutarwace kuma illa ce babba. Hasalima Allah na fushi da irin wadannan mazaje masu aika irin wannan mugun danyen aiki.
Akwai matar da ta taba kirana ta waya tana korafi a kan yadda mijinta ya shafe wata da watanni ba tare da ya yi kwanciyar aure da ita ba. Ta nuna a gaskiya mijinta yana son ya jefa ta cikin mummunan yanayi, don har ta fara tunanin fita waje. Ta ce a gaskiya ita mai tsananin bukata ce, alhali mijinta ba ya kusantar ta, don haka idan sha’awa ta dame ta takan rasa yadda za ta yi. Ta ce ta kai kararsa a wajen magabata amma abin ya ci tur. Ta ce da ta ga abin ya ki ci, ya kuma ki cbinyewa ne sai ta zaunar da mijinta kuma ta nemi ya saketa, idan kuwa ya ki yarda to za ta rika fita tana yin lalata da wasu mazan a waje. Ta nuna wa mijin cewa ta sanar da shi haka ne, don ta lura bai damu da halin da ya jefata a ciki ba, kuma ya sani duk alhakin da ta debo a waje, to yana da kamasho. Nan take mijin hankalinsa ya tashi, da ya fahimci ba zai iya biya mata bukata ba, sai ya rabu da ita cikin sauki. Daga nan ne ta sake wani sabon auren, kuma ta nuna yanzu Alhamdulillah, sabon mijinta yana biya mata bukata a bangaren kwanciyar aure daidai gwargwado.
Wannan labari ya nuna da an samu macen da ba ta jin tsoron Allah, me kake ganin zai faru. Na san akwai dimbin mata da yanzu haka suke fuskantar irin wadannan mummunan yanayi daga wajen mazajensu na aure. Ya kamata maza masu irin wannan hali su ji tsoron Allah, su sani matan da suke aure amana ce da Allah Ya damka musu, kuma idan suka ci amana, Allah Zai tambaye su a ranar gobe kiyama. Duk matar da ka san ba za ka iya biya mata bukata a ibadar aure ba, ka rabu da ita cikin lumana, don ya zama babu cuta kuma ba cutarwa.
Wata kuwa cewa ta yi, da ta fahimci mijinta bai iya biya mata bukata, takan saci jiki ne ta fita waje tana haduwa da tsohon saurayinta, wanda tun farko shi ta so ta aura amma iyayenta suka ki amincewa. Ta ce shedan ya ribace ta, don sun shafe lokaci mai tsawo suna lalata da wannan tsohon saurayi nata ba tare da sanin mijinta ba. Ta nuna daga baya Allah Ya shirye ta gane abin da suke yi ba zai harfar musu da mai ido ba inda ta nemi mijin ya sake ta, kuma ya ba ta takardarta. Ta ce bayan ta yi wani auren ne ta samu kwanciyar hankali inda yanzu haka ta haifi ’ya’ya uku. Ita ma ta yi kira ga mazajen da ke cutar da matansu a wajen kwanciyar aure da su yi hattara, don komai na iya faruwa.
Za mu ci gaba
Za a iya samun Ahmed Garba a 08028797883