✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmanci da hukunce-hukuncen noma a Musulunci (2)

Hudubar Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo, Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi   Huduba ta Daya Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,…

Hudubar Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo, Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi

 

Huduba ta Daya

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Wanda Yake zubo mana ruwa daga sama zubowa, sannan Ya tsattsage kasa tsattsagewa, sai Ya tsirar da kwaya daga cikin kasar da inabi da ciyawa da zaitun da itacen dabino da lambuna masu yawan itace; duk dai domin jin dadinmu da na dabbobinmu! Ya Ubangijinmu! Godiya gareKa kadai take, kamar yadda ya dace da girman zatinKa da kuma girman ikonKa! Ya Allah! Ka yi salati ga shugabanmu Muhammad bawanKa, kuma ManzonKa; Annabin nan da bai koyi karatu da rubutu daga wani mutum ba da jama’ar gidansa da sahabbansa; kuma Ka dawwamar da aminci a gare shi.

Bayan haka, ya ku ’yan uwa na imani! Ba mu gushe ba, muna magana kan muhimmanci da hukunce-hukuncen sana’ar noma a Musulunci. A yau, in Allah Ya so, za mu karfafa zancenmu da zantuttuka da nazarce-nazarcen masana kimiyyar wannan dadaddiyar sana’a da na cibiyoyinta da kungiyoyinta a takaice (kari a kan nasihohin da suka gabata da wadanda za mu ambata insha Allah). To ga wasu daga cikin fa’idoji da muhimmancin sana’ar noman:

1. Samar da abinci da abin sha ga kai da iyali da kasa da duniya baki daya. Wannan abinci domin mutane da dabbobi da tsuntsaye da kwari ne. Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “To, mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa mana. Lallai ne Mu, Mun zubo ruwa zubowa. Sa’annan Muka tsattsage kasa tsattsagewa. Sa’annan Muka tsirar da kwaya a cikinta. Da inabi da ciyawa. Da zaitun da itacen dabino. Da lambuna masu yawan itace. Da ’ya’yan itacen marmari, da makiyaya ta dabbobi. Domin jin dadi a gare ku da dabbobinku.” (Abasa:24-32)

Kuma masana tattalin arziki na cewa duk kasar da ke iya ciyar da jama’arta da kanta, to, ta magance kashi 40 cikin 100 na matsalolinta. Ai kun san cewa kowane magidanci, idan ya magance matsalar abinci a gidansa, to, ai duk sauran matsaloli suna da sauki! Sai abinci ya samu, sa’annan ake samun kwanciyar hankali da lafiya (tunda yunwa ma hadari ce ga lafiya) da zama lafiya da tsaro!

2. Samar da arziki (kudin-shiga) da kuma aikin yi: Kamar yadda muka fada a baya, noma wata babbar hanya ce ta samar da aikin yi da arziki ga kai da iyali da kasa baki daya. Wannan tabbataccen abu ne da kowa zai iya shaidawa, musamman a irin wannan jihar tamu ta Kebbi da sauran jihohin da suka rungumi noma gadan-gadan! Kana ganin yadda, alhamdu lillahi mutane ke samun kudi ta hanyar noman shinkafa da rake da kankana da albasa da sauransu – har suna biyan kudin aikin Hajji albarkacin noman nan! Da ma Hausawa sun ce “Noma tushen arziki!”

Samun wannan alheri ba abin mamaki ba ne tunda da ma ayoyin Alkur’ani Mai girma, kamar yadda muka ambata a baya, sun nuna cewa ruwan saman nan arziki ne – wato arziki na nan cikin amfani da ruwan sama – a yi noma da sauransu. Allah Ya sa mu dace. Kuma, sanannen abu ne a tarihin kasar nan (Najeriya), kamar yadda masana suka fada, cewa bayan samun ’yancin kai a shekarun farko a kasar nan, noma ne yake samar da kashi 60 cikin 100 na kimar kayayyaki da ayyukan da kasar take samarwa a shekara (GDP)). Haka kuma noman ne yake samar da kashi 80 cikin 100 na kudin shiga ta hanyar hajojin da kasar ke fitarwa zuwa waje. (Magaji, 2016 da Graham, 2017), wato abin da a Turance ake kira Edport Earnings.

Wata manuniya game da yadda noma yake samar wa jama’a aikin yi ita ce irin yadda manyan masana’antu masu sarrafa kayan amfanin gona suke wannan gaggarumin aiki. Misali, wannan babban kamfanin ko masana’anta ta casar shinkafa wato ‘WACOT Rice Ltd’ da ke Argungu, an kiyasta cewa za ta iya samar wa mutum 3,500 ayyukan yi; tsakanin masu aiki kai-tsaye a cikinta da masu aikin da ke dangantaka da ita. (Ado, 2017). To, wannan daya fa ke nan cikin dubu! Lissafa sauran ire-irensa (gaba dayan masu sarrafa kayan amfanin gona) ka gani, manyansu da kananansu; ma’aikata nawa za ka samu a kasar nan? Masu iya magana sun ce: “Gulbi ka wuce kwalfewa!”

To, haka dai sana’ar noma take samar da aikin yi da kudin shiga ga duk wanda ya dukufa a kan kowane mataki da bangare nata; kama daga samar da iri ko abin dashe da samar da kayan aikinsa da lebaranci a cikinsa da ayukkan binciken masana da na kere-keren kayan aiki ko injunan sarrafa amfaninsa da aikin sarrafawar kansa da kasuwanci a cikin sha’aninsa da sauransu. Walillahil-hamd.

3. Samar da kayan sarrafawa ga masana’antu. Masana sun sani cewa sana’ar noma ce ke samar da kayan sarrafawa (raw materials) ga masana’antun da ke sarrafa kayan abinci da abin sha da na magungunna da na tufafi da na takardu da jakunkuna da robobi da katako da sauransu. (Gotomo, 2017). Na yi imani cewa, idan aka matsa bincike, za a lura da cewa da yawa, ko mafi yawan kayayyakin da muke amfani da su a yau da kullum – ko a gida ko a makaranta ko a ofis ko a masallaci ko a ina, ba za su rasa alaka da sha’anin noma ba!

Kai, amfanonin fa suna da yawa! Ya wajaba mu gode wa Allah, ya ku ’yan uwa! Kada mu manta da zancenSa Madaukaki da Y ace: “Lallai idan kun gode, hakika, Ina kara muku, kuma lallai ne idan kun kafirta, hakika azabaTa, tabbas, mai tsanani ce.” (Ibrahim:7)

Ya Allah, Ka taimaka mana ga ambatonKa da gode maKa da kyauatata ibadarKa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Huduba ta Biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu, Annabi Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, a ci gaba da ambaton abin da ya saukaka game da hukunce-hukuncen Musulunci kan wannan sana’a mai albarka – wato sana’ar noma, za mu takaita bayananmu insha Allah a cikin wadannan ’yan kalmomi:

1. An so mutum ya ce “Ma sha Alahu la kuwwata illa billah” a lokacin da zai shiga gonarsa. Malam Abubakar Jabir Aljaza’iri ya fadi a littafin tafsirinsa “Aisarut-Tafasir” a sharhin tafsirin zancen Allah Madaukaki cewa: “Kuma me ya sa lokacin da ka shiga gonarka (ba) ka ce ‘Ma sha Allahu laa kuwwata illa billah’ (Abin da Allah Ya so (shi ke tabbata) babu wani karfi face tare da Allah) ba?…” (Al-Kahf:39) – Ya ce, Imam Malik (Allah Ya yi masa raham) ya ce: “Ya kamata duk wanda zai shiga gidansa ko gonarsa ya ce: ‘Ma Sha Allahu la kuwwata illa billah.’ Mai tafsirin Raddul Azhan Ila Ma’anil Kur’an ya ce, a bayanin wannan ayar dai: “Ya zo a Hadisi cewa: ‘Duk wanda a ka bai wa wani alheri na iyali ko duniya, a kan haka ya ce ‘Ma sha Allahu la kuwwata illa billah, ba zai ga abin kyama ga abin nan ba.”

2. Neman halal farilla ne. Don haka manomi ya kudirta cewa yana sauke nauyin da ke kansa ne na farillar neman halal da kuma samun albarkar da ke ciki. Malam Abdullahi Dan Fodiyo (Allah Ya yi masa rahama) ya fadi a littafinsa “Kitabun-Niyyati…” cewa:

“ i. Manomi ya yi niyyar neman halal, saboda biyayya ga Hadisin da ya ce: “Neman halal farilla ne a kan kowane Musulmi bayan farilla.” Wato bayan farillar Imani da kuma Sallah.

i. Kuma manomi ya yi niyyar samun rokon gafarar mala’iku ta hanyar noman nan; saboda abin da ya tusgo na cewa mala’iku suna rokar wa manomi gafarar Allah matukar shukarsa tana koriya (tsanwa).

ii. Kazalika, manomi ya yi niyyar wadatuwa daga rokon mutane ta hanyar noman da yake yi; saboda Hadisin da ke cewa: Wani mutum ya ce: “Ya Manzon Allah! Ka aza ni a kan aikin da zan yi in shiga Aljanna, sai (Annabi SAW) ya ce (masa): “Kada ka roki kowa komai.”

3. Haka kuma, wajibi ne mutum ya fitar da Zakka ga duk abin da ya noma wanda shari’a ta shar’anta a fitar masa da Zakka – irin su hatsi da masu kayau-kayau (irin su wake) da sauransu; kamar yadda shari’a ta tsara a fitar da Zakkar. Allah Ya sa mu dace.

Sa’annan kuma, wajibi ne manoma su nisanci wadannan abubuwa da kan faru lokacin ayyukan noma:

1. Walakanta Sallah – rashin yin ta cikin lokaci (cikin jama’a) ko kuma rashin yin Sallar kirki.

2. Tsiraici – (wato rashin suturta gaba dayan abin da ke tsakanin cibiya zuwa gwiwa – ga namiji). Misali mutum ya kasance daga shi sai gajeren wando kawai; wai aiki yake yi! To, babu sabani game da haramcin wannan, inji Sheikh Abdullah bn Fodiyo, a “Kitabun Niyyati.”

3. Yaudara ko kissar aikin da ’yan aiki (lebarori) sukan yi a wajen aikin da aka dauke su su yi (wato irin abin da ake kira ‘ja-rufe’ ko keta ko kuma duk nau’in mugun aiki ba bisa kuskure ba). Ai kowa ya san cewa yaudara haramun ce a Musulunci.

4. Shan kwaya don karin karfi (ba da umarnin likita ba). Karshenta, mutum zai je ya cutar da kansa ko  lafiyarsa ta hakan. Alhali kuwa Musulunci ba ya maraba da duk abin da zai cutar da rayuwa ko lafiya.

5. Cin iyaka a kan zalunci da rashin gaskiya. Hakika, ya zo a cikin Hadisi cewa: “Wanda duk ya debi yankin kasar wani (misali gonar wani ko gidan wani) a kan zalunci, koda gwargwadon taku guda ne, to, za a yi masa sakandami (a rataya masa a wuyansa) da abin da ya diba na zalunci har zuwa kasan bakwai (a Ranar Kiyama).” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi.). Allah Ya kare mu.

Bari mu tsaya a nan, duk da yake ba iyakar bayanan ke nan ba.

Allah    Ya amfanar da ni da ku da abin da muka fada ko muka ji. Ya Allah! Ka kyautata al’amurran Musulmi a ko’ina a duniyar nan. Ya Allah! Duk wanda yake son ya dagula mana lissafi, kada Ka ba shi sa’a, kuma ka dagula masa nasa lissafin, domin karfin ikonKa.

Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa baki Daya. Wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo (MNSE, MNIAE) ya gabatar da wannan huduba ce a ranar Juma’a 15 ga Zul-Hajji, 1440 (16/08/2019) a Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi, za a iya samunsa ta tarho mai lamba: 08181059714 da 08036049452